Matar gwamna ta rabawa dubban mata kuɗi da kayan Sallah a Zamfara

Uwar gidan Gwamnan jihar Zamfara Hajiya Aisha Muhammad Bello Matawalle ta raba wa mata sama da dubu biyar (5000) kayan Sallah da kuɗi a jihar domin shagulgulan Sallah.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata takardar sanarwa da jami’ar yaɗa labaran matar gwamnan, Zainab Shu’aibu Abdullahi ta fitar a Gusau a ranar Talata.
Da take jawabi wurin taron ƙaddamar da raba kayayyakin, shugaban mata na jam’iyar PDP ta jihar Hajiya Aisha Waziri ta yabawa Hajiya Aisha Matawalle bisa ƙirƙiro da shirye-shirye da dama na tallafawa mata. Tana mai cewa tunda Gwamna Matawalle ya dale kujera yake baiwa mata kulawa ta musamman.
Ita ma a nata bangare, mai baiwa gwamna shawa kan harkokin mata Hajiya Fatima Musa ta bayyana dacewan tallafin da matar gwamnan ta rabawa mata a daidai lokacin daidai wannna lokaci.
Ta ƙirayi al’ummar Zamfara da su ci gaba da baiwa gwamnatin Matawalle haɗin kai domin ciya da jihar gaba.
Da take gabatar da tallafin ga waɗanda suka rabauta a Gusau a ranar Talata, Hajiya Aisha Bello Matawalle, ta ce ta raba kayan ne domin taimakawa mata domin yin shagulgulan sallah.
Ta ce kayan an raba ne ga mata da aka zakulo daga kananan hukumomin Gusau, Tsafe da Bundugu a ƙudurin gwamnatin mijinta na tallafawa rayuwar marasa ƙarfi.
Daga ƙarshe ta nemi al’ummar jihar da su yi amfani da wannan lokaci na Sallah domin yin adu’o’in neman agajin Allah a lamuran da suka shafi tabarbarewar tsaro da Najeriya ke fuskanta.