Masu nuna maitar takarar shugaban ƙasa ba tare da la’akari da tsarin karɓa-karɓa ba, sun ɗibge da kwaɗayin mulki -Uzor Kalu

Tsohon Gwamnan Jihar Abiya, kuma Bulalar Majalisar Dattawa a yanzu, Uzor Kalu, ya ce masu fitowa tun yanzu su na nuna maitar son tsayawa takarar shugaban ƙasa, ba tare da yin la’akari da tsarin karɓa-karɓa ba, to ba su san abin da su ke yi ba.

Sannan kuma ya ce ya cancanci iya “riƙe mulkin Najeriya idan shekarar 2023 ta zo, sai dai kuma ya ƙara da cewa amma ba bakin rai bakin fama ya ke neman zama shugaban ƙasa ba.

Haka dai Kalu ya shaida wa manema labarai a Majalisar Dattawa, a ranar Laraba.

Kalu wanda ya nuna sha’awar fitowa takardar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin APC, ya ce zai fito ne kawai idan APC ta damƙa takarar ga yankin Kudu maso Gabas.

A ranar 26 Ga Fabrairu ne APC za ta yi Taron Gangamin Jam’iyya na Ƙasa, inda za a damƙa takarar ga yankin da ake so ya fito.

“Duk mai shisshigin neman takarar shugabancin ƙasa a yanzu, ba tare da yin la’akari da tsarin karɓa-karɓa, to ba da gaske ya ke yi ba, kuma bai yi wa ‘yan Najeriya adalci ba. ” Inji Kalu.

“Duk wanda ke da gaske, kuma ya san abin da ya ke yi, to zai jiya sai ya yankin da aka bai wa takarar tukunna. Idan yankin sa ne, dai ya fito.”

Farkon makon jiya ne Premium Times ta buga labarin da Kalu ya ce “zan fito takarar shugaban ƙasa, idan APC ta damƙa wa Kudu maso Gabas takara.”

Yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke ƙaratowa cikin 2023, Bulalar Majalisar Dattawa, Orji Kalu ya bayyana cewa zai fito takarar shugabancin Najeriya, idan har jam’iyyar APC ta damƙa takarar ga yankin Kudu maso Gabas, wato yankin ƙabilar Igbo.

Haka tsohon Gwamnan na Jihar Abia ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai (NAN), yayin komawar sa Abuja, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, a ranar Talata.

NAN ta ruwaito Kalu na cewa ƙungiyoyi da dama sun nemi Kalu ya fito takarar shugabancin ƙasa, kuma sun bayyana cewa a shirye su ke domin su tabbatar cewa ya yi nasara a zaɓen 2023.

Sannan kuma an ga fastocin Kalu na neman takara an manna a kan titinan jihohin ƙasar nan da dama.

Yayin da ya ke yaba wa ƙungiyoyin da ke neman ya fito takara, mawallafin jaridun The Sun ya ce gani su ka yi shi ne ya fi cancanta, shi ya sa kowa ke rububin sa.

Ya ce tabbas shi ma ya ga fastocin sa sun cika garuruwa shi ya ƙara masa ƙwarin guiwar neman fitowa takara.

Sai dai ya ce shi zai yi biyayya ga jam’iyyar APC mai mulki. Saboda takarar sa na da sharaɗin cewa sai idan APC ta damƙa wa Kudu maso Gabas takara, sannan zai fito gadan-gadan.

“Ina mai godiya ga jama’a masu mammanna fastoci na a garuruwan Najeriya. Ni ban ce zan tsaya takara ko ba zan tsaya ba. Amma dai idan aka damƙa takara ga Yankin Kudu maso Arewa, to tabbas zan fito gadan-gadan.

“Amma dai na san cewa jam’iyyar mu za ta tsayar da ɗan takarar da zai haɗa kan Najeriya. Kuma dama hakan shi ne mafi muhimmanci ga ɗorewar ƙasar nan.” Inji Kalu.