Raba a Facebook
Tura zuwa Twitter
Masu garkuwa da mutane sun ƙara koma hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin, inda suka yi awon gaba da matafiya da dama.
Majiyoyi sun ce lamarin ya afku a ƙasa da kilomita biyar daga inda maharan suka gudanar da irin wannan ta’asa a ranar Lahadi.
Lawan Sani, wani ganau da ya bi hanyar bayan faruwar lamarin ya ce ya ga akalla motoci huɗu da babu kowa a ciki kuma akwai fashe-fashe a jikin gilashin da kuma tayoyin motocin, Daily Nigerian ta ruwaito.
Sai dai ba a samu jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
-
Facebook
Twitter