Masu garkuwa sun ƙara komawa hanyar Kaduna, sun sace matafiya da dama

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Masu garkuwa da mutane sun ƙara koma hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin, inda suka yi awon gaba da matafiya da dama.

Majiyoyi sun ce lamarin ya afku a ƙasa da kilomita biyar daga inda maharan suka gudanar da irin wannan ta’asa a ranar Lahadi.

Lawan Sani, wani ganau da ya bi hanyar bayan faruwar lamarin ya ce ya ga akalla motoci huɗu da babu kowa a ciki kuma akwai fashe-fashe a jikin gilashin da kuma tayoyin motocin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sai dai ba a samu jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

  • Facebook

    Twitter

Labarin bayaGwamnatin Jihar Neja ta hana sayar da babura

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce da ke da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jarida.