MARTANIN GWAMNATI GA ATIKU: ‘Idanun tattalin arzikin Najeriya garau su ke, ba su fama da dundumi’ -Lai Mohammed

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa furucin da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya yi cewa tattalin arzikin Najeriya na fama da ciwon dundumi, kuma gab ya ke da makancewa, ba gaskiya ba ce, farfaganda ce kawai don ya razana jama’a.
Atiku ya yi wannan iƙirarin na durƙushewar tattalin arzikin Najeriya, a lokacin da ya ke gabatar da Daftarin Ceto Tattalin Arzikin Najeriya da zai yi kamfen ɗin takarar shugaban ƙasa da shi, kwanan baya, a Legas.
A lokacin ƙaddamarwar ce har Atiku ya ce idan aka zaɓe shi a 2023, to a cikin kawanakin 100 na farkon shugabancin sa zai danƙara Naira tiriliyan 10 cikin tattalin arziki, lamarin da ya janyo masa raddi, ana tambayar sa inda zai samo kuɗaɗen.
A martanin da Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya mayar wa Atiku, a wurin taron manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, ya ce tabbas Najeriya na fuskantar ƙalubalen tattalin arziki, amma maganar a ce wai tattalin arzikin ya kusa durƙushewa ko kuma a yi masa kallon idanun da su ka kusa makancewa, ƙarya ce, ba gaskiya ba ce.
“Tattalin arzikin Najeriya bai kusa durƙushewa ba, tattalin arzikin Najeriya kamar tofa ya ke, ya yi juriya sosai, domin a 2016 da 2020 ya tsallake siraɗin durƙushewa.”
Lai ya ci gaba da bayyana irin dajin da tattalin arzikin Najeriya ya keto a ‘yan shekarun nan, da kuma yadda ya farfaɗo albarkacin wasu nagartattun tsare-tsare da gwamnatin tarayya ta bijiro da su.
Sannan kuma Lai Mohammed ya ƙaryata zargin da Atiku ya yi cewa tun da APC ta kafa gwamnati cikin 2015, “a duk shekara sai an samu giɓi cikin kasafin kuɗi.”
“Zargin Atiku ba gaskiya ba ce. Ba daga 2015 ne aka fara samun giɓi cikin kasafin kuɗi ba. An fara samun wannan giɓin tun cikin 2009, lokacin da ma ake sayar da gangar ɗanyen mai guda ɗaya dala 100.”
Daga nan kuma Lai Mohammed ya riƙa lissafa irin manyan ayyukan da Gwamantin Tarayya ta yi a faɗin ƙasar nan, inda ya ƙarƙare da cewa “surutan da Atiku ya yi, ai ba wani sabon abu ya faɗa ba.”