Mahaifiyata ta kara min karfin guiwar shiga gasar – In ji Aisha Dalil garzuwar gasar Hikayata ta 2021

Kamar yadda BBC Hausa ta saba yi duk shekara na baiwa mata damar shiga gasar rubutun gajerun labarai a bana ma ta yi haka inda ta bayyana mutum uku da suka yi zarra a cikin dubban rubutu da suka shiga gasar.

A bana ma an zabi mutum uku da labaran su suka yi fice cikin dubban rubutun da aka yi ta aikawa a lokacin da aka bude rumbun shiga gasar.

PREMIUM TIMES HAUSA ta tattauna da wadanda suka yi nasara a gasar na bana.

Aishatu Musa Dalil ita ce ta yi nasara a gasar ta 2021 a inda labarinta mai suna ‘Haƙƙina’ ya yi nasarar zuwa na daya a gasar.

Labarin Haƙƙina labari ne kan wata matashiya mai suna Fatima wadda mijin mahaifiyarta ya yi mata dukan kawo ‘wuka’ tare da fyaɗe har ya ji mata raunuka masu muni.

“ Mahaifiyata da yayata suka bani kwarin gwiwar shiga wannan gasa. Na kan yi rubutu ne kawai don nishadi sai a wannan karon suka ce in shiga gasar har gashi cikin dubban labarai na yi ne a gaba.

” Yanzu na samu karfin guiwar yin rubutu sosai kuma ina kira ga yan uwana mata su maida hankali sosai wajen yin rubutu.

Aishatu mai shekaru 18 tana shekararta ta farko a sashen koyon Ingilishi da Faransanci a Jami’ar Umaru Musa Ƴar’adua a jihar Katsina.

Wacce ta zo na biyu Nana Aicha Hamissou Abdoulaye ƴar asalin jihar Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa burin ta shine ta yi rubutun da zai amfani jama’a.

” Burina shine in yi rubutun da zai amfani jama’a. Labarin da za a rika tinkaho da shi a duk lokacin da aka karanta shi.

Sai kuma Zulaihat Alhassan wadda ita ma mazauniyar jihar Kaduna ta ce wannan ba shi bane karon farko da ta shiga gasar ba.

” Na fara shiga gasar hikayata ne a shekarar bara sai dai ban yi nasara ba sai a bana. Kira na ga mata marubuta shine su maida hankali matuka wajen yin rubutu da zai amfanar da Al’umma.”

Zulaihat ta kara da cewa wannan nasara da ta samu zai kara mata karfin guiwa ne wajen ci gaba da rubuce rubuce domin amfanin A’umma.

Gasar Hikayata ta bana

A bana kuwa, mata uku ne su fafata wajen darewa kujerar gwarzuwar gasar Hikayata – wanda suka hada da Nana Aicha Hamissou Abdoulaye ƴar asalin jihar Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar da Zulaihat Alhassan ƴar jihar Kaduna a Najeriya da Aishatu Musa Dalili ita ma ƴar jihar Kaduna a Najeriya.

Wadda ta yi nasarar zuwa ta ɗaya a gasar za ta samu kyautar kuɗi dala dubu biyu ($2,000) da lambar yabo. Wadda ta zo zo ta biyu za ta samu lambar yabo da kyautar kuɗi dala dubu ɗaya ($1,000), ita kuma wadda ta zo ta uku za ta samu kyautar kuɗi dala ɗari biyar ($500) da lambar yabo.

BBC Hausa ta samar da gasar Hikayata ne don ƙarfafa wa mata marubuta guiwa da kuma haɓaka rubutu a harshen Hausa.

Shugaban Sashen Hausa na BBC, Aliyu Tanko ya ce “gasar ta kasance wata turba ga mata marubuta wurin fito da batutuwan da suka shafe su da zaƙulo hanyoyin matsalolin da suke fuskanta. Kuma mu dama fatanmu kenan.”

Ita ma jagorar alƙalan gasar a bana Dokta Hauwa Bugaje ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta ce “kullum mata marubuta a ƙasar Hausa ƙara gogewa suke yi saboda damarmaki irin wannan gasa da ake ba su. A bana mun ga labarai masu nagarta, kuma wannan na nuna cewa kwalliya na biyan kuɗin sabulu.”