Ma’aikatan ofishin Buhari da na Osinbajo sun yi rantsuwar kaffarar daina bayyana sirrin gwamnati

Babban Sakatare na Fadar Shugaban Ƙasa, Tijjani Umar, ya ja kunnen ma’aikatan ofishin Shugaba Muhammadu Buhari da na Mataimaki, Yemi Osinbajo su guji fallasa sirrikan ofis da duk wasu bayanan da ba a bada iznin bayyanawa a duniya ba.

Umar ya yi masu wannan gargaɗi a ranar Talata yayin da su ke ɗaukar rantsuwar kaffarar daina bayyana sirrin ayyukan ofis da ba a so a bayyana.

Aƙalla ma’aikata 42 ne su ka yi wannan rantsuwar a gaban Mai Shari’a Hamza Muazu na Babbar Kotun FCT Abuja.

Babban Sakataren ya gargaɗe su cewa aikata irin wannan bayyana ayyukan sirri na ofis fa babban laifi ne, kuma akwai hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama ya na aikata haka.

“Zan fara bayani na da cewa wanann rantsuwa fa ita ce fa ita ce matakin farko na yin abin da ke daidai bisa ƙa’ida a ofisoshin ku.

“Karya dokar ofis ta hanyar fallasa bayanan sirri laifi ne babba, domin ya na tauyewa da kawo naƙasu wajen gudanar da ayyukan a gwamnati.

“To dalili kenan mu ka ga ya kamata mu taimaki waɗannan ɓangaren ma’aikata ta hanyar rataya masu layar rantsuwar kaffara. Saboda su ne ke kula da bayanan sirri na gwamnati.

“Haka kuma mu na so jaddada masu tare da gsrgaɗin su kan muhimmancin ɓoye waɗannan bayanai da kuma hukuncin da ke tattare da duk wanda ya fallasa waɗannan bayanai.”

“Waɗanda su ka yi rantsuwar sun haɗa da na Ofishin Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Ofishin Sakateriyar Shugaban Ƙasa, ma’aikatan Ofishin Tattara Rajista na Mataimakin Shugaban Ƙasa, ma’aikatan Tattara Rajista na Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa da kuma na ofishin Babban Sakatare na Ofishin Shugaban Ƙasa.”

Ya ce za a ci gaba da yin wannan rantsuwa akai-akai.

Duk da an shar’anta masu yin wannan rantsuwa, Muazu ya ce har yau dai ba a samu ko ma’aikaci ɗaya ya fallasa wani bayani na sirri ba.