Lambobin waya miliyan 70 ne ba su da rajistar banki (BVN) a Najeriya – Shugaban eTranzact

An nuna damuwar cewa aƙalla layukan waya miliyan 70 ne ba a haɗa su da lambar ajiyar banki ba, wato BVN.

Shugaban Kamfanin Hada-hadar Zamani na eTranzact, Niyi Toluwalope ne ya bayyana haka a Lagos.

Toluwalope ya yi wannan iƙirarin a lokacin da ya ke jawabi a Taron Shekara-shekara na Ƙungiyar ‘Yan Jarida Masu Aika Rahotannin Hada-hadar Kasuwanci ta Najeriya (CAMCAN), taro na 24 da aka shirya a Legas.

Ya ce mutum miliyan 150 a cikin mutum miliyan 200 duk su na da waya a Najeriya.

“Waɗannan mutane miliyan 150 su na da layuka miliyan 110. Amma daga cikin su, layuka miliyan 40 ne kaɗai aka haɗa da rajistar lambar ajiyar banki ta BNV.”

Toluwalope ya ƙara da cewa layuka miliyan 70 duk haka nan su ke ziƙau, ba a haɗa su da kowace lambar BVN ba.

A kan haka ne ya ce akwai matuƙar buƙatar janyo miliyoyin mutane masu ƙananan harkoki su rungumi tsarin ajiya a banki, su buɗe asusu tare da lambobin wayoyin su.

Ya ce yin hakan zai taimaka wajen bunƙasa ƙananan kasuwanci da ma manyan harkokin baki ɗaya.

Ya ce kamata ya yi a tashi tsaye a zaburar da masu ƙananan kasuwanci ko sana’o’i alfanun tsarin hada-hadar zamani wajen bunƙasa tattalin arziki, ta hanyar amfani da bankuna a sauƙaƙe.

Har yanzu dai ƙofa a buɗe ta ke wajen yi wa layukan wayoyin rajista, tare da haɗa su da lambar BVN ta banki.

Ita lambar BVN, sai idan ka buɗe asusun ajiya a banki za ka iya mallakar ta.