Lamarin ya fi ƙarfin mu, ba mu iya rage farashin gas ɗin girke-girke -Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana cewa lamarin tsadar gas ɗin girke-girke ya fi ƙarfin ta, ba za ta iya saukar da farashin tsadar da ya yi ba.

Gwamnati ta ce dalili shi ne gas ɗin girke-girke ba ya cikin man da gwamnatin tarayya ke biya wa kuɗaɗen tallafi.

“Saboda kasuwannin duniya ke daidaita farashin gas ɗin girke-girke, kuma ba ya cikin man da ake biya wa tallafi.”

Karamin Ministan Fetur Timipre Sylva ne ya bayyana haka, ganin yadda ‘yan Najeriya ke fama da matsin-lambar tsadar gas, har ta kai akasarin gidaje yanzu an koma girki da gawayi ko itace da ƙiraruwa.

Sai dai kuma Sylva ya ce amma gwamnati za ta duba ta ga ko akwai wani abu da za ta iya yi a kan lamarin.

Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya (International Energy Agency) ta ce tsadar farashin gas a Turai na da nasaba da farfaɗowar da tattalin arzikin ƙasashe ya fara yi, buƙatar sa da ake yi a yanzu fiye da wanda ake samarwa, sai kuma matsanancin sanyin hunturu da ake yi a wasu sannan Turai.

Cikin shekara dai farashin gas ya nunka fiye da sau ɗaya a Najeriya, har ta kai gidaje da dama sun daina amfani da gas, sun rungumi gawayi da ƙiraren itatuwa.

Yayin da Sylva ke amsa tambayoyin manema labarai a ranar Talata a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce wani dalili da ya ƙara haddasa tsadar gas a cikin Najeriya, shi ne harajin-jiki-magayi (VAT), wanda aka ɗora a kan gas.