KWALARA: Mutum 46 sun mutu cikin mako daya a Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Ƙasa (NCDC), ta bayyana cewa mutum 46 sun mutu a cikin mako daya a dalilin kamuwa da cutar amai da gudawa a kasar nan.

NCDC ta bayyana wannan ƙididdiga a shafin ta na yanar gizo ranar Talata bisa ga rahotannin yaduwar cutar da ta samu daga jihohi 36 da Abuja.

Rahotan ya nuna cewa adadin yawan mutanen da cutar ta kashe an gano su ne daga jihohi 8 a kasar nan.

Jihohin sun hada da Borno-13, Sokoto-12, Katsina-8, Bauchi-6, Niger-3, Kaduna-2, Adamawa-1 da Kano 1.

Hukumar ta ce bisa ga rahotan da ta samu daga ranar 30 ga Agusta zuwa 5 ga Satumba ya nuna cewa a jihohi 25 da Abuja tun da aka shiga shekaran 2021.

Mutum 1,677 sun kamu da cutar a cikin mako daya a jihohi 12 inda hakan ya kawo jimlar yawan mutanen da suka kamu da cutar zuwa mutum 69,925 a kasar nan.

Jihohin da mutum 1,677 suka kamu sun hada da Bauchi-566, Katsina-282, Sokoto-258, Yobe-183, Borno-179, Niger-94, Kaduna-66, Adamawa-34, Gombe-8, Kano-4, Kebbi-2 da Nasarawa-1.

A jimla mutum 69,925 sun kamu da cutar sannan mutum 2,323 sun mutu daga jihohi 25 a kasar nan.

Jihohin sun hada da Adamawa, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ekiti, Enugu, FCT, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger, Osun, Plateau, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara.

Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin cewa NCDC ta bayyana cewa daga ranar 2 Ga Satumba, 2021, ƙididdiga ta tabbatar da cewa cutar kwalara ta kashe mutum 2,141 kuma mutum 65,145 ne su ka kamu da cutar a cikin jihohi 23 da Gundumar FCT Abuja.

Ga dalilai 10 dake haddasa barkewar cutar a kasar nan

1. Rashin tsafta da barin ƙazanta a gida, musamman abinci da kayan abinci ko kwanukan cin abinci.

2. Zubar da tulin shara da bola aikin unguwanni, wadda ruwan sama ke maida ƙazantar ta s cikin jama’a.

3. Zubar da shara ko bola ko bayan gida a cikin ƙaramu da magudanan ruwa.

4. Yin bayan gida a fili ko a kan bola.

5. Rashin ruwa mai tsafta a cikin al’umma.

6. Ƙarancin asibitocin kula da marasa lafiya a cikin jama’a marasa galihu.

7. Ƙaranci ko rashin magungunan da za a bai wa mai cutar kwalara cikin gaggawa.

8. Matsalar ƙarancin jami’an kiwon lafiya a cikin jama’a.

9. Rashin hanyoyi masu kyau da za a garzaya asibiti da mai cutar amai da gudawa cikin gaggawa.

10. Shan ruwan ƙarama ko kogi, wanda ake zubar da shara, kashin dabbobi da kuma bayan gida.