KUƊAƊEN SATA: Najeriya na farautar £2 biliyan da aka jibge a wasu ƙasashen waje -Minista Malami

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ta bayyana cewa ta gano aƙalla wasu kuɗaɗen sata har fam biliyan 2 da ta ke ƙoƙarin karɓowa daga ƙasashe daban-daban na duniya.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana haka, inda ya ce kuɗaɗen waɗanda a naira sun kai naira tiriliyan 1.12, idan aka canja £1 zuwa N560 a farashin gwamnati, su na daga cikin kadarorin da Najeriya ke ƙoƙarin ƙwatowa a ƙasashe daban-daban, ciki har da Birtaniya da Ireland.

“Mu na ta ƙoƙarin ganin mun dawo da wasu fam biliyan 2 da wasu kadarorin maƙudan kuɗaɗe a ƙasashe daban-daban. Kuma mu na tsara wasu bincike da ganawa domin dawo da wasu kuɗaɗen da kadarori a Birtaniya, waɗanda wasu su ka saci kuɗaɗe su ka kimshe a can, ta hanyar sayen kadarori.” Inji Malami.

Minista Malami ya yi wannan bayani ga manema labarai a gefen Taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 76 da ke gudana yanzu haka a New York, a Hedikwatar UN a Amurka.

Kakakin Yaɗa Labarai na Minista Malami mai suna Umar Gwandu ne ya watsa wannan bidiyo, wanda Malami ya yi wannan bayani ga ‘yan jaridu.

Ministan ya ƙara bayyana cewa Gwamnatin Najeriya ta a cikin shekaru huɗu da su ka gabata, an karɓo dala miliyan 700 na kuɗaɗen satar da aka jida daga Najeriya, aka kimshe a ƙasashen waje.

Don haka Malami ya ce Gwamnatin Tarayya ta na ta ganin cewa ta cimma matsaya da sauran ɓangarori domin karɓo fam biliyan 2 daga wasu ƙasashe.

Sai dai kuma Malami bai yi cikakken bayani dalla-dalla ba.

“Ba na son bayar da labarin dalla-dallar abin da ake ciki dangane da wannan ƙoƙarin da mu ke yi, domin magana ce ake yi ta ƙarƙashin ƙasa, ba ta fito fili ba tukunna.”

Da ya ke magana a kan ‘yan Najeriya masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda, Minista Malami ya ce ba zai bayyana ko su wane ne ba a yanzu, saboda a kan bincike ake har yanzu.