KOWA TA SA TA FISSHE SHI: Yadda Buhari da likitocin Najeriya su ka ƙaurace wa asibitocin ƙasar nan lokaci guda

Kamar jira su ke yi Shugaba Buhari ya tafi Landan ganin likita, su kuma Ƙungiyar Likitoci ta NARD sai su ka tsunduma yajin aikin da su ƙaurace wa asibitocin ƙasar nan, ko allura su ka daina yi wa majiyyata.

A makon da ya gabata dai Shugaba Buhari ya yi kwanaki fiye da 200, jimlace a Landan da sunan zuwa ganin likita, a tsawon shekaru shida da ya shafe a kan mulki.

Asibitocin ƙasar nan da dama sun wayi garin Litinin da yajin aikin likitocin da ke ƙarƙashin ƙungiyar NARD. Wakilan PREMIUM TIMES sun zagaya asibitoci a garuruwa daban-daban, kuma sun tabbatar da haka.

A Asibitin Gwamnantin Tarayya na Legas da ke Ebute-Metta, wakilin mu ya samu likita ɗaya tal ya ganin marasa lafiya sama da 300, a ranar Litinin ɗin da aka fara yajin aikin.

Wani da ya zanta da shi, ya ce ya kai matar sa asibitin ne, kuma ita ce ta 45 a layi. “Amma kuma har zuwa yanzu ƙarfe 3 na yamma ba a zo kan ta ba. Wasu ma duk sun koma gida a fusace, kuma cikin damuwa.” Inji Inanaco.

A Abuja kuwa, wakilin mu ya leƙa Babban Asibitin Ƙasa, wanda Najeriya ke ji da shi, kuma na fita-kunya.

Wani mai suna Lucky Oche da ke jiyyar mahaifin sa, ya shaida wa wakilin mu cewa marasa lafiya a asibitin hankulan su a tashe ya ke. “Saboda kowa tsoro ya ke ji idan yajin aikin ya daɗe, za a sallami da wanda ya ji sauƙi da wanda bai ji ba, duk a sallame su baki ɗaya.”

Kusan haka lamarin ya ke a yawancin asibitocin ƙasar nan tun daga ranar Litinin, kuma alamomi na nuna cewa lamarin ya na ci gaba da dagulewa.

Likitocin dai sun tafi yajin aiki ne saboda gwamnatin tarayya ta ƙi cika masu alƙawarin da ta ɗauka tun cikin watan Afrilu, bayan sun shafe watanni a baya su na gargajiya kafin a kai ga ɗaukar alƙawarin.