Kotu ta yanke wa mutumin da ya yi wa ƙanwar matarsa fyaɗe ya saka mata kanjamau a Jigawa hukuncin ɗauri rai da rai

Babban kotu dake Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa ta yankewa wani mutum mai suna Idris Munkaila hukuncin zaman gidan yari na har abada bayan ta kama shi da yi wa surukansa mai shekara shida fyade.
Idris yayi lalata da kanwan matarsa da kuma sanya mata cutar Ƙanjamau da yake ɗauke da ita.
Dama kuma an tilasta shi ya aure matarsa ne bayan ya yi lalata da ita ya saka mata Ƙanjamau wanda hakan yayi sanadiyar lalacewar aurenta da masoyinta na farko.
Kakakin ma’aikatar Sharia ta Jihar Jigawa, Zainab Baba-Santali ce ta bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma’a.
Ta ce Munkaila, ɗan asalin garin Sara ne dake Karamar Hukumar Gwaram kuma ya aikata laifin ne a shekarar 2017 amma an yi masa hukunci a 2021.
Mai Shari’a, Musa Ubale shi ne ya yankewa Munkaila hukunci a karkashin dokar penal code na Jihar Jigawa mai lamba 283.
Baba-Santali ta ce Munkaila ya yaudari yarinyar ne da alawa kafin yayi lalata da ita kuma ya gargaɗi yarinyar kada ta kuskura ta fadawa kowa abin da yayi mata.
Amma bayan kwana biyu sai uwar yarinyar ta fara ganin wani farin ruwa yana fitowa daga gaban yarta, daga nan ta fallasa sunan Munkaila cewa shi ne yayi lalata da ita.
Nan take sai uwar yarinyar ta garzaya zuwa asibiti domin duba lafiyar yarinyar inda aka gano cewa lallai an yi lalata da ita kuma har Munkaila ya saka mata Kanjamau.