Kotu ta raba auren wasu ma’aurata saboda tsananin kiyayya da suke wa juna

Fasto Adekunbi Osho mai shekara 45 ya samu biyan bukatar sa bayan kotun dake Igando a jihar Legas ta raba auren sa na shekara shida da matarsa Rebecca.

Alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya warware kullin wannan auren ne bayan dagewar da fasto Osho ya yi na lallai kotu ta raba aurensa duk da rokon da aka yi ta yi.

A bayanin da ya yi Osho yace matarsa Rabecca ta ki jinin ta ga mijinta na ci gaba a rayuwa da wurin aikinsa.

Ya ce zargin fasikancin da Rabecca ta yi masa ya sa ba a yi masa ganin mutumin kirki ballantana a kara masa girma a wurin aiki.

“Rabecca ta rubuta wasika ga fastocin cocin da nake aiki da su da shugaban cocin cewa ni kasurgumin manemin matane sannan ta yi min sharri wai na taba aika mata da yan iska su kashe.

“Wata rana Rabecca ta taba dalla min mari ta kuma yayyaga mun riga a cikin jama’a saboda wai ta kama ni da wata mata.

Osho ya ce Rabecca masifaffiyar mata kuma bata kaunar ‘yan uwansa hatta yar su daya da suka haifa ma bata so ya kusance ta.

Ya ce ya gaji da auren kuma yana rokon kotu ta bashi damar kula da ‘yar ta su guda daya mai shekara 3 da suka haifa tare.

Rabecca mai shekara 36 ba tace komai ba game da hujojjin da mijinta ya bada a kotun.

Sai dai ta ce ta hana Osho taba ‘yar su ne saboda ba shine mahaifinta ba.

“Wani saurayi na ne ya yi mun ciki a lokacin da nake auren Osho da hakan ya sa bazan bari ya goya dan wani ba.