Kotu ta gurfanar da Sojan Saman da ya yi gaban kansa da naira miliyan 20 da aka yi kuskuren danna masa a asusun bankin sa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC reshen jihar ta maka wani sojan sama mai suna Haruna Samuel a babban kotu a Kaduna dalilin ka,a gaban sa da yayi da wasu kudade har naira miliyan 20 da ma’aikatar sa ta yi kuskuren loda masa a akant bisa kuskure.

Samuel ya ce tabas ya ga kudin tashiga asusun bankinsa amma kuma suna shiga ya tattara su ya ci gaba da hidimar sa ganin cewa kudin daga wurin aikin sa a ka turo su.

Kakakin hukumar Wilson Uwujaren ya ce abinda Samuel ya yi sata ne kuma ya saba wa tsarin dokar kasa ne. Ya ce abinda ya kamata shine ya maida kudin a lokacin.

Uwujaren ya ce an kama Samuel ajihar Filato kuma ta shigar da kara a kan sa a Kotu domin a kwato kudin.

Samuel bai amsa laifi ba.

Lauyen da ya kai kara Precious Onyeneho ya yi kira ga alkalin kotun da ya tsayar da ranar da za a yi ainihin zaman shari’ar.

Lauyen Samuel S.A Yahaya ya nemi kotun ta bada belin Samuel.

Alkalin kotun Darius Khobo ya bada belin Samuel akan Naira miliyan 5 tare da gabatar da shaida daya dake da fili a jihar Kaduna.

Khobo ya ce hukumar EFCC da rajistatan kotun za su tabbatar da ingancin filin.

Za a ci gaba da shari’a ranar 10 ga Maris.