Kotu ta bada umarnin a saki ZakZaky da matarsa

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Wata babbar kotu a Kaduna ta bada umurnin a saki jagoran Shi’a ta (IMN) Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenatu Ibrahim tare da wanke su daga dukkanin zarge-zargen da ake musu.

Kotun ta bada umurnin ne a zamanta na yau Laraba a yayin yanke hukuncin shari’ar wadda aka kawashe tsawon shekaru biyu ana yinta.

Kotun ta kawo ƙarshen wannan shari’ar ne bayan babban Malamin ya kwashe sama da shekaru 6 a tsare gidan yari.