Kotu ta bada belin barawon da ya sace wa wata makauniya waya da ‘yan kudinta

Kotun majistare dake jihar Legas ta bada belin barawon da ya saci wayar salula da tsaban kudi har Naira 5,000 a gida wata makauniya a kan Naira 100,000.

Kotun ta kama Adewale Oladeji mai shekara 39 da laifin sata, hada baki da abokinsa domin su yi sata da balle kofar gidan wannan makauniya.

Shi dai Oladeji ya musanta aikata haka.

Lauyan da ya shigar da karar Simeon Uche ya ce Oladeji da abokinsa da ya tsare suka shiga gidan wata makauniya mai suna Roseline Aiguh dake lamba 5 layin Ebunoluwa a Ojo ranar 11 ga Nuwamba.

Uche ya ce a wannan rana Oladeji da abokinsa sun shiga gidan matan saboda suna tunanin ta yi tafiya bata nan a gida.

“Da suka isa gidan sai Oladeji ya sa abokinsa ya shiga gidan domin ya kwaso musu kaya shi kuma ya na tsaye a waje yana gadi.

“Sai dai kafin su ankare makwabtan Roseline suka dira musu inda suka kama Oladeji sannan abokinsa ya bi ta saman kwanon dakin ya gudu.

“An tsinci wayan salula da farashin da ya kai Naira 50,000 da kudi Naira 5,000.

Alkalin kotun Ademola Adesanya ya bada belin Oladeji akan Naira 100,000 sannan da shaidu biyu.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 21 ga Janairu 2022.