Kotu na kokwanton lafiyar ƙwaƙwalwar Abduljabbar

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Wata kotun shari’a da ke shari’ar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ta umarci a yi masa gwajin kwakwalwa da kunne a wani zaman ci gaban shari’ar da ake yi masa a birnin Kano.

Majiyar mu ta BBC ta ruwaito Kotu ta bayar da umarnin ne bayan Malamin ya gaza amsa tambayoyin da alƙalin kotun Mai Shari’a Sarki Ibrahim Yola ya yi masa ranar Alhamis.

An gurfanar da malamin ne bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.

  • Facebook

    Twitter

Labarin baya“Na shuka alkhairin da za ku riƙa tunawa da ni bayan na tafi” Shugaba Buhari

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce dake da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jaridu.