Korona ta yi ajalin mutum 21 ranar Litinin a Najeriya – NCDC

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta bayyana cewa cutar Korona ta kashe mutum 21 ranar Litinin a Najeriya.

Hukumar ta kuma ce a wannan rana mutum 387 ne suka kamu da cutar a jihohi 15 da Abuja.

A ranar Lahadi mutum 365 ne suka kamu da cutar, mutum 8 sun mutu a jihohi 7 da Abuja.

A ranar Asabar Najeriya ta samu karin mutum 547 mutum 2 sun mutu a jihohi 14 da Abuja.

Zuwa yanzu mutum 199,538 ne suka kamu da cutar, an sallami mutum 188,427.

Mutum 2,619 sun mutu sannan har yanzu mutum 8,492 dake dauke da cutar.

Yaduwar cutar korona a Najeriya

Legas – 75,204, Abuja-20,954, Rivers-11,483, Kaduna-9,366, Filato-9,252, Oyo-8,540, Edo-5,945, Ogun-5,332, Kano-4,131, Akwa-ibom-4,185, Ondo-3,968, Kwara-3,672, Delta-3,201, Osun-2,818, Enugu-2,675, Nasarawa-2,426, Gombe-2,333, Katsina-2,212, Ebonyi-2,048, Anambra-2,108, Abia-1,860, Imo-1,784, Bauchi-1,567, Ekiti-1,658, Benue-1,487, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,074, Bayelsa-1,125, Niger-968, Sokoto-796, Jigawa-568, Yobe-501, Cross-Rivers-542, Kebbi-458, Zamfara-253, da Kogi-5.

Gwamnati ta cire kasar India daga jerin kasashen da aka yi wa katanga da Najeriya

Gwamnatin tarayya ta cire kasar India a jerin kasashen da ta hana mutane daga kasar nan zuwa sannan da mutane daga can zuwa Najeriya saboda yaduwar sabuwar samfurin korona dake yi wa mutane kisan faradɗaya, wato nau’in ‘Delta Variants’.
Shugaban kwamitin PSC Boss Mustapha ya ce gwamnati ta cire kasar ne bayan ganin nasarorin da kasar ta samu wajen rage yaduwar cutar.
Zuwa yanzu kasar India ta yi nasarar rage yaduwar cutar korona a kasar domin a watan da ta gabata mutum ƙasa da 40,000 ne suka kamu da cutar a kasar.