Korona ta kwararo Legas da Abuja, mutane da dama sun kamu ranar Asabar

Alkaluman yaduwar cutar korona da hukumar NCDC ta fitar ya nuna cewa Korona fa ta danno gadan-gadan inda ta kama mutane da dama a jihar Legas da babban birnin tarayya, Abuja.

Sakamakon gwajin cutar da aka yi na ranar Asabar ya nuna cewa daga ranar 21 zuwa 24 ga Yuni mutum 247 sun kamu da cutar a kasar nan.

Bisa ga sanarwar da hukumar NCDC ta yi ranar Asabar sakamakon gwajin cutar ya nuna cewa mutum 203 ne suka kamu da cutar a jihar Legas saura kuwa an gano su ne daga Abuja da wasu jihohi uku a Kasar nan.

Zuwa yanzu mutum 256,958 ne suka kamu sannan cutar ta yi ajalin mutum 3,144 a kasan.

Har yanzu mutum 3,637 na dauke da cutar sannan mutum 250,177 sun warke.

Duk da gabatar da wannan sakamakon da hukumar ta yi hukumar ba ta yi karin haske kan dalilin da ya sa cutar ke ci gaba da yaduwa ba da kuma dalilin da ya sa jihar Legas ce ta fi fama da yaduwar cutar ba.

Mutum 17 ne suka kamu a babban birnin tarayya Abuja, jihar Rivers 14, Cross Rivers 12 da Kano 1.

Tun bayan bullowar cutar a shekarar 2020 mutum 100,125 ne suka kamu a jihar Legas, mutum 28,738 a Abuja, mutum 16,761 a jihar Rivers.