Korona ta kashe mutum 68 a ranakun Asabar da Lahadi, amma ko a jikin ‘yan Najeriya

Cutar korona ta sake darkako Najeriya da kisa, inda a ranar Asabar ta kashe rayuka 35, ranar Lahadi kuma ta ɗauki rayuka 33.

Hukumar NCDC ce ta bayyana mutuwar mutum 33 a ranar Lahadi da dare, cikin jawabin da ta fitar.

Adadin na nufin mutum 68 kenan cutar ta kashe a Najeriya a cikin kwanaki biyu.

Zuwa yanzu korona ta kashe mutum 2837 a Najeriya, tun farkon ɓarkewar cutar.

Sai dai kuma har yanzu babu wata alama da ke nuna cewa ko gwamnatin tarayya za ta ɗauki wani tsauraran mataki ko matakai a jihohin da cutar ta fi yin kisa.

Yayin da cutar ta darkako da kisa, an daina jin ƙarajin hukumomin da abin ya shafa su na kamfen din hanyoyin daƙilewa ko guje wa kamuwa da cutar, musamman a cikin game-garin al’umma.

Hukumomi sun fi maida hankali ga masu shigowa cikin Najeriya daga filayen jiragen ƙasa, musamman na Lagos da Abuja, inda a can ne aka fi ɗaukar tsauraran matakai.

Duk da kisan da korona ke yi, a cikin Najeriya musamman a kasuwanni da wuraren tarukan siyasa ko bukukuwa, an daina ɗaukar matakan bada rata a tsakanin mutum da mutum.

Su kan su jama’a akasari sun yi watsi da bin ƙa’idojin kare kai daga kamuwa da cutar korona, musamman a wuraren mu’amala, hada-hada, masallatai da coci-coci.

Duk wani ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen ganin an daƙile cutar korona, ya daina samun yabo a wurin mafi yawan ‘yan Najeriya. Ko dai saboda haushin yadda ake zuzuta korona, amma kuma an kasa daƙile ‘yan bindiga masu kisa, garkuwa da tarwatsa mutanen karkara daga garuruwan su.

Ko kuma saboda halin ƙuncin tsadar rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki, inda akasarin kayan abinci da na masarufi duk farashin su ya nunka farashin da can baya kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki.

Har yanzu masu ƙaramin ƙarfi da talakawa masu neman cin yau da na gobe, ba su ma san inda ake yin allurar rigakafin korona ba.

Idan ma sun san wurin, to sun yi biris da ita. Ko don saboda neman abincin da ya gigita su, ko kuma saboda har yanzu an kasa cusa masu dalili ko hujjar da za su amince a yi masu rigakafin.

Da dama kuma wasu sun yi watsi da batun korona, saboda haushin yadda su ke jin labarin gwamnati ta raba biliyoyin kuɗaɗe da kayan abincin tallafin korona, amma kuma su ko wanda ya karɓa ba su taɓa gani ba.