Korona ta kashe mutum 44 a Jihar Akwa Ibom

Gwamnatin Jihar Akwa Ibom ta yi kira ga al’ummar jihar cewa cutar korona gaskiya ce, don haka kada su bari wasu gafalallu su cuce su, har su ƙi ɗaukar matakan kariya.

Da ya ke jawabi a wurin Taron Bikin Shagulgulan Kirsimeti na ƙabilar Eket, Mashawarci na Musamman Ga Gwamna Emmanuel Udom a Fannin Kiwon Lafiya, Dominic Ukpong ya ce zuwa yanzu dai korona ta kashe mutum 44 a jihar tun daga farkon ɓarkewar annobar a ranar 1 Ga Afrilu, 2020.

“Jama’a kada mu kuskura mu bari wasu gafalallu su su riƙa yi mana huɗubar ƙaryata korona, su cuce mu a banza. Domin korona gaskiya ce.

“A Ƙaramar Hukumar Uyo ce korona ta fi yin kisa, sai nan Ƙaramar Hukumar Eket sai kuma Ikot Ekpene.

“Kwanaki uku da su ka gabata an samu ɓullar cutar korona a jikin mutum biyar. Amma dai har yanzu ana ƙoƙarin gano shin nau’in ‘Omicron’ ce, ko kuwa a’a?”

Wannan bayani na sa ya zo daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa korona nau’in ‘Omicron’ ta ɓulla a Najeriya.

Tuni dai Majalisar Tarayya ta gargaɗi Hukumar NCDC da Ma’aikatar Harkokin Lafiya ta Tarayya cewa fa su shantake har cutar ta kai ga fara kisa a Najeriya.

Haka nan ƙasar Birtaniya da Canada sun ƙara wa’adin hana matafiya daga Najeriya shiga ƙasashen.