KORONA TA GAMU DA KIMIYA: Chana ta kirkiro maganin shaƙe ta hanci maimakon allura don rigakafin Korona

Chana ta amince a fara amfani da maganin shaƙen daƙile cutar korona na farko, a matsayin agajin gaggawa ga mai ɗauke da cutar.

Kamfanin Tianjin mai suna CanSino Biologics ne ya ƙirƙiro maganin, wanda Hukumar Kula da Ingancin Magunguna ta Chana ta amince da shi a ranar Lahadi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ce amincewar ke da wuya har hannun jarin CanSino ya ƙaru da kashi 7% washegari a ranar Litinin.

Yayin da ake amfani da sauran magungunan korona ta hanyar allurar riga-kafi, wannan sabon magani ba allura ba ce, shaƙa za a riƙa yi.

Sai dai kuma kamfanin ya ce ba a san ranar da maganin zai shiga kasuwa har a fara amfani da shi ba. “Saboda akwai wasu hukumomin da tilas su ma sai an jira sun amince da shi tukunna.

Daga 2020 zuwa yanzu dai Chana ta amince da allurar rigakafin korona har nau’i takwas. Sai wannan magani na shaƙe shi ne cikon na 9.

Hukumar Lafiya ta Duniya dai ta ce zuwa ranar 31 Ga Agusta, an yi wa mutum biliyan 3.4 allurar rigakafin korona a duniya.

WHO ta ce daga ranar 3 Ga Janairu, 2020 zuwa 3 Ga Satumba, 2022, mutum miliyan 6,477,468 ne su ka kamu da korona a Chana. Kuma a cikin su mutum 24,883 ne cutar ta kashe a cikin ƙasar.

A ranar Asabar da ta gabata a kafa dokar kulle a kudancin birnin Shenzhen da kudu maso yammacin Chengdu, inda aka killace mutum miliyan 21 a gida tun daga ranar Alhamis.