Korona ta dawo Najeriya, ta kama mutum 29 cikin mako ɗaya – NCDC

Hukumar NCDC ta tabbatar da cewa mutum 29 sun kamu da cutar korona tsakanin 7 Ga Janairu zuwa 13 Ga Janairu.

Wani alƙaluman bayanan da NCDC ta fitar a ranar Lahadi, ya tabbatar da cewa an samu mutanen da su ka kamu da cutar a cikin jihohi biyar, da kuma babban birnin tarayya, FCT Abuja.

Hakan na nufin har yanzu adadin waɗanda korona ta kashe a Najeriya har yanzu ya na nan a mutum 3,155.

Sai dai adadin waɗanda su ka kamu ne ya tashi zuwa mutum 259,858.

Ya zuwa 10 Ga Janairu, mutum miliyan 5,708,974.

Babban Daraktan NCDC na ƙasa, Ifedayo Adetofa ne ya bayyana haka.

Ɓullar korona cikin ƙasar nan ya haifar da kariyar tattalin arziki a Najeriya da duniya baki daya, tun lokacin da ta fara ɓulla a cikin 2020.