KORONA NAU’IN ‘OMICRON’: Birtaniya da Canada sun hana kowane ɗan Najeriya shiga ƙasashen su, sai yadda hali ya yi

“Daga ranar Litinin, ƙarfe 4:30 na yamma, Gwamnatin Birtaniya ta hana kowane ɗan Najeriya shigowa ƙasar nan. Amma ‘yan asalin Ingila da Ireland da su ka je Najeriya, za su iya dawowa. Kuma tilas su na shigowa su killace kan su.”

Wannan ne jawabin da Ministan Harkokin Lafiya na Birtaniya, Sajid Javid ya yi a ranar Lahadi.

Birtaniya dai ta bi sahun ƙasar Kanada ta ƙara wa’adin hana shiga ƙasar ta daga Najeriya, sakamakon hauhawan ɓullar korona nau’in ‘Omicron’ a Najeriya.

Ƙasar dai cewa ta yi ya zama tilas ta ɗauki matakin tun da wuri.

Ita kuwa Kanada hatta duk wani matafiyi matsawar dai ya biyo ta Najeriya, to ta haramta masa shiga ƙasar.

Birtaniya ta ce za ta yi amfani da wannan lokacin haramcin shiga ƙasar daga Najeriya ta ƙara yin nazarin yadda cutar ke fantsama da kuma irin matakan bai-ɗaya da ya kamata ƙasar ta ɗauka.

A ranar Talata ce Majalisar Tarayya ta gargaɗi NCDC da Ma’aikatar Lafiya kada su yi wasa da rayukan jama’a.

Majalisar Tarayya ta gargaɗi Hukumar NCDC cewa ta tsaurara binciken-ƙwaƙwaf tare da ɗaukar matakai a kan masu shigowa cikin ƙasar nan.

Wannan gargaɗi ya zo ne a ranar Talata, ranar da NCDC ta bayyana ɓullar cutar korona nau’in ‘Omicron’, wadda aka samu ƙwayoyin cutar a jikin wasu matafiya biyu da su ka shigo daga Afrika ta Kudu.

Majalisar ta kuma yi kakkausan kira ga Mai’aikatar Harkokin Lafiya ta Tarayya cewa kada ta tsaya jan-ƙafa har cutar ta fara fantsama a cikin ƙasar nan.

Majalisar ta yi wannan kiran bayan amincewa da ba’asin da Ɗan Majalisar Tarayya Dachung Bagos (ɗan PDP daga Jihar Filato) ya yi a lokacin zaman majalisa, ranar Talata.

Baya ga Najeriya, wasu ƙasashen da cutar korona nau’in ‘Omicron ta ɓulla, sun haɗa da: Birtaniya, Belgium, Botswana, Jamus, Italiya, Hong Kong, Isra’ila, Jamhuriyyar Czech, Netherlands, Denmark da Austaraliya.

Tuni dai manyan ƙasashen duniya sun hana shiga ƙasar su daga ƙasashen Kudancin Afrika, waɗanda su ka haɗa da Afrika ta Kudu, Botswana, Eswatini, Lesotho, Malawi, Mozambique, Nsmibiya da Zimbabwe.

A ranar Talata ce NCDC ta sanar cewa wasu matafiya biyu sun shigo da mummunar korona samfurin ‘Omicron’ cikin Najeriya.

Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa (NCDC) ta bayyana cewa cutar korona samfurin Omicron mai saurin maƙure mutum ta kashe, ta shigo Najeriya.

Cikin jawabin da Babban Daraktan NCDC, Ifedayo Adetifa ya fitar a ranar Talata da dare, ya ce an samu wasu matafiya mutum biyu da su ka shigo da cutar daga Afrika ta Kudu.

Ya ce an tabbatar da haka ɗin bayan wani gwaji da aka yi a Babban Ɗakin Gwajin Abuja.

Wannan sanarwa ta zo ne kwanaki biyu bayan ƙasar Kanada ta bayyana cewa an matafiya biyu daga Najeriya ɗauke da cutar korona samfurin Omicron a Kanada.

A kan haka, NCDC ta ce ta ƙara miƙewa tsaye wajen tsaurara matakai.

Sannan kuma ta na ƙara kira da a gaggauta zuwa ana yin rigakafin korona.

Wannan jarida a ranar Talata ta buga labarin cewa Samfurin ‘Omicron’ mai saurin maƙure mutum ta kashe ba ta iso Najeriya ba.

Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa (NCDC) ta bayyana cewa sabuwar korona mai saurin maƙure mutum ta kashe farat ɗaya ba ta shigo Najeriya ba.

Sabuwar cutar ta korona samfurin Omicron (SARS-Cov-2) dai a yanzu ta tashi hankulan duniya, inda a na ta ɓangaren Najeriya ta haramta wa ‘yan ƙasar nan shiga ƙasahe irin su Afrika ta Kudu, Botswana, Italy, Jamus, Belgium da Birtaniya, inda cutar ta ɓulla.

Cikin wata sanarwa da NCDC ta fitar raanr Asabar da dare, Darakta Janar na hukumar, Ifedayo Aderifa ya ce cibiyar NCDC na sa-ido tare da lura da halin sa ake ciki kada cutar ta shammaci ƙasar nan.

Ya ce kuma duk halin da NCDC ke ciki, za ta riƙa sanar da jama’a

Omicron: Korona Mai Saurin Kisa: NCDC ta ce har yanzu dai babu wani rahoton wannan sabuwar cuta ta yi kisa a Najeriya, amma fa an gano sagwangwaman ta har guda 126.

“Gano sagwangwaman wannan sabuwar cuta tare da gami da fantsamar cutar a Afrika ta Kudu, hakan ya tabbatar da cewa wannan cutar ta na saurin yaɗuwa a cikin mutane.

Amurka Da Turai Sun Ƙaƙaba Wa Ƙasashen Afrika Takunkumin Hana Zirga-zirga Cikin Su:

Wasu fitattun ‘yan Najeriya ciki har da Shugaban Bankin Bunƙasa Afrika (AIB), Akinwumi Adesina, sun yi tir da yadda Turai da Amurka su ka ƙaƙaba wa Afrika dokar shiga ƙasashen su, saboda an samu bayyanar cutar korona samfurin Omicron ta ɓulla a Afrika ta Kudu.

Alakija wadda ita ma ta yi wannan tir ɗin a hirar ta da BBC, ta ragargaji ƙasar Amurika da Turai bisa yi wa sauran ƙasashen Afrika kudin-goro, ake gallaza masu a kan laifin da ba kowace daga cikin su ta aikatawa ba.

“Alƙaluman masu bincike ya nuna cewa korona samfurin Omicron da ta ɓulla a Afrika ta Kudu, ta na saurin kama jikin mutum, kuma ta kan yi kisan farat-faɗa.” Inji Hukumar Kula da Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WHO).

Baya ga Afrika ta Kudu, korona samfurin Omicron, ta bayyana a ƙasashen Isra’ila, Malawi, Botswana, Birtaniya, Jamus, Italy, Belgium, Hong Kong da wasu ƙasashe da dama.