KORONA: Mutum 30 sun kamu da cutar a Najeriya a karshen mako

Bayan kwanaki hudu da da aka yi mutum 13 kacal suka kamu da cutar korona, hukumar NCDC ta sanar cewa an samu karin mutum 30 da suka kamu da cutar ranar Lahadi.

An samu wadannan mutane a jihohi shida da Abuja.

Waɗanda aka samu sun kamu kuwa ɗalibai ne dake rubuta jarabawar JAMB.

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa wasu wuraren rubuta jarabawar sun ki kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da korona inda wasu wuraren rubuta jarabawar na bari dalibai na shiga ba tare da sun saka takunkumin fuska ba.

Cutar korona

Hukumar NCDC ta ce zuwa ranar Lahadi mutum 255,796 ne suka kamu, cutar ta yi ajalin mutum 3,143 sannan har yanzu mutum 2,709 na dauke da cutar.

Mutum 249,920 sun warke daga cutar.
Gwamnati ta Yi amfani da kwalaben maganin rigakafin korona guda 38,399,067 wajen yi wa mutane allurar rigakafin cutar a kasar nan.

Yaduwar cutar

Zuwa yanzu jihar Legas ce jihar da ta fi fama da yaduwar cutar domin alkaluman yaduwar cutar da aka fitar na ranar Lahadi ya nuna cewa mutum 12 ne suka kara kamuwa da cutar a jihar

Daga nan sai Abuja inda mutum shida suka kamu.
Jihar Kaduna ta samu Karin mutum 5 da suka kamu daga ranar 28 zuwa 29 ga Afrilu.

Jihohin Rivers -2, Bauchi-2, Kano-2 da Delta-1.