KORONA: Gwamnati ta cire kasashen Afrika ta Kudu, Brazil da Turkiyya daga cikin jerin kasashen da aka yi wa katanga da Najeriya

Gwamnatin tarayya ta cire kasashen Afrika Ta Kudu, Brazil da Turkiya daga jerin kasashen da ta hana mutane daga kasar nan zuwa sannan da mutane daga can zuwa Najeriya saboda yaduwar sabuwar samfurin korona dake yi wa mutane kisar faradɗaya, wato koron mai nau’in ‘Delta’.

Shugaban kwamitin PSC Boss Mustapha ya sanar da haka yana mai cewa gwamnati ta yanke wannan shawara ne bayan ta duba irin nasarorin da kasashen suka samu wajen dakile yaduwar cutar a kasashen su

Saka dokar hana wasu kasashe zuwa Najeriya

Idan ba a manta ba a ranar biyu ga Mayu gwamnati ta sanar da saka dokar yi wa ‘yan Najeriya katanga da kasashen Brazil, India da Turkiya.

A watan Yuni gwamnati ta saka kasar Afrika ta Kudu cikin jerin wadannan kasashe.

A lokacin gwamnati ta ce ta yi haka ne saboda ta dakile yaduwar sabuwar samfurin korona dake yi wa mutane kisan faradɗaya, wato nau’in ‘Delta Variants’.

Bisa ga dokar duk dan Najeriya da ya dawo daga wadannan kasashe sai ya killace kan sa na tsawon kawanaki 14 kafin ya fara cudanya da mutane ko yawo a cikin gari.

Bayan haka a watan Satumba gwamnati ta cire kasar India daga jerin kasashen.

Sai dai kafin hakan ya faru gwamnati ta kwace takardun fasfo din wasu matafiya ‘yan Najeriya 2000.

Gwamnati ta kwace fasfo din su ne bayan bijire wa dokar da gwamnati ta saka kan balaguro zuwa kasashen da ta yi wa iyaka da kasar nan a wancan lokaci.