KORONA: Daga mutum kasa da 40 da ake samu, ranar Talata yawan wadanda suka kamu ya zarce 100

Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa, NCDC ta bayyana cewa mutum 102 suka kama cutar ranar Talata.

NCDC ta buga adadin yawan mutanen a shafin ta dake yanar gizo a safiyar Laraba.

A ranar Litini hukumar ta bayyana cewa mutum 49 be suka kama cutar sannan a ranar Alhamis mutum 122 suka kamu.

Alƙalumar ranar Talata sun nuna cewa mutum 68 sun kamu a jihar Ondo, Bayelsa -17, Kaduna -5, Legas -3, Rivers -3, Akwa-ibom -2, Gombe-2, Ebonyi-1 da Oyo-1.

uwa yanzu Mutum 163,269 sun warke, mutum 2,117 sun mutu, mutum 1,542 na killace a wurin kula da masu fama da cutar a Najeriya.

Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin cewa gwamnatin Najeriya na farautar sama da mutum 200, wadanda su ka shugo ƙasar nan, amma su ka sulale ba tare da tsayawa an kullace su ba.

A dalilin haka gwamnati ta Yi kira ga ƴan Najeriya da su nesan ta kan su da wadannan mutane, kada su kamu da Korona.

Zuwa yanzu dai mutum miliyan ɗaya kacal aka yi wa rigakafin korona a Najeriya, ƙasa mai yawan jama’a kusan miliyan 200.

Matsalolin da ƙasar ke fuskanta wajen yaƙi da korona, sun haɗa har da rashin yarda akwai cutar a Najeriya da wasu ke nunawa.