KOKARIN KWACE KUJERAR GWAMNAN KANO: Kwankwaso da ƴan jam’iyyar NNPP sun gudanar da sallar rokon samun nasara

Dan takarar shugaban kasa na NNPP kuma jagorar Kwankwasiya, Rabiu Kwankwaso, da gwamnan Jihar Abba Yusuf, tare da ƴaƴan jam’iyyar NNPP na Kano, sun gudanar sa addu’ar neman nasara a Kotun sauraren kararrakin zabe da ke zama a Kano.
Jam’iyyar NNPP ce ta yi nasara a zaben gwamna da na shugaban kasa a jihar Kano. Sai dai tun bayan wannan nasara jam’iyyar APC mai mulki ta garzaya kotun sauraren karrarrakin zaɓe domin kalubalantar nasarar da NNPP ta yi.
Sai dai kuma ga dukkan alamu wankin hula zai kai wa NNPP dare domin cikin su duk ya ɗuri ruwa ganin alamun kamar kotu za ta kwace kujerar ta baiwa APC, kujerar da Nasiru Gawuna ya yi takara a kai.
A ranar Asabar, duka ilahirin ƴan kwankwasiyya sun yi dafifi a filin ido inda suka gudanar da sallar rokon Allah ya ba jam’iyyar nasara a hukuncin da kotu ke shirin yanke wa nan ba da dadewa ba.
Cikin abubuwan da APC ke ƙalubalanta a gaban kotu sun hada da kcancantar Abba Yusuf yin takarar gwamnan a Kano a jam’iyyar NNPP, da kuma korafin wai an yi aringizon kuri’u da ba a saka musu tambarin Hukumar Zabe ba.
Sai da ita ma NNPP, ta roki kotu kada ta saurari wannan lara domin baya cikin abinda ya kamata kotun ta saurara har ta yanke hukunci a kai.
Ana sa ran za a yanke hukuncin nan da kwanaki kaɗan.