KO ZA TA IYA KUWA?: Dogayen shingayen 25 da Najeriya za ta tsallake a zaɓen 2023

* A ranar 25 Ga Fabrairu ce Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a Sabuwar Dokar Zaɓe. Hakan ya buɗe kofar saura shekara ɗaya kenan dindi a yi zaɓen Shugaban Ƙasa, wanda zai maye gurbin Buhari.

* Za a zaɓi shugaban ƙasa a ranar 25 Ga Fabrairu, 2023, zaɓen jihohi kuma a ranar 11 Ga Maris, 2023.

* INEC ta gindaya sharuɗɗan cewa tilas zuwa 3 Ga Yuni, 2022, kowace jam’iyya ta fitar da ‘yan takarar ta.

* Za a yi wannan zaɓe a lokacin da ake fama da matsalar tsaro, tattalin arziki da kuma ruɗanin siyasa a Afrika ta Yamma, inda sojoji su ka maida hankali su na juyin mulki.

* A fannin tattalin arziki, Najeriya ta samu kan ta cikin ƙarancin kuɗaɗen shiga, sakamakon hawa da saukar da farashin fetur ke yi, matsalar kasa haƙo wanda ake buƙata, batun tattalin kuɗaɗen mai, wanda ya ke neman kashe tattalin arziki, kuma ya haifar da ƙarancin kuɗaɗen shiga.

* Gwamnatin Buhari na kashe kusan kashi 90% bisa 100% na kuɗaɗen shigar ta wajen biyan basussuka.

* Hakan ya sa ƙasar na amfani da basussukan da ta ke ci a cikin gida da na wasu ƙasashen kuma ta na yin ayyukan da su ka sauƙaƙa da su.

* Bugu da ƙari, yayin da male-malin bashi suka cika wa Najeriya tulun cikin ta har iya wuya, matsalar rashin aikin yi sai ƙara ta’azzara ta ke yi, har ta kai kashi 35 bisa 100 na majiya ƙarfi a Najeriya ba su da aiki.

* Gefe ɗaya kuma kayan rayuwa da kayan masarufi sai tsawwala tsada su ke yi a lokacin da kuɗaɗen da jama’a ke samu ke ta raguwa.

* A siyasance, Najeriya na fama da matsalar Biafra da Oduduwa masu son ɓallawa daga ƙasar, waɗanda su ba su ma ƙi ba idan ƙasar ta dare kafin zaɓen 2023.

* Matsalar tsaro da aikata muggan laifuka sai ƙaruwa su ke ta yi, tun bayan zaɓen 2019 a Najeriya.

* A Arewacin Najeriya ‘yan ta’adda sun kashe ɗimbin rayuka kuma sun lalata dukiyoyin jama’a ba adadi. Ga kuma ‘yan bindiga waɗanda a yanzu kusan ma sun fi Boko Haram aikata munanan ɓarna.

* A Kudu ma muggan laifuka sai ƙaruwa su ke yi, ga kuma garkuwa da mutane ana biyan su maƙudan kuɗaɗen fansa sun cika ko ina a faɗin Najeriya.

* Yayin da an kusa ƙure ƙoƙarin da sojoji ke yi, su kuma ‘yan sanda na buƙatar garambawul tun daga sama har ƙasa.

Zaɓen 2023 dai zai maida hankali ne wajen ganin shin APC mai mulki ke za ta samar da shugaban 2023 ko kuwa PDP, wadda ta yi mulki a baya shekaru 16?

* A APC dai an fi maida hankali wajen yaɗa ji-ta-ji-tar tsaida Bola Ahmed Tinubu, Tsohon Gwamnan Legas. Sai dai kuma ana ta yamaɗiɗi da shi kan zargin ba shi da ƙoshin lafiya, kuma ko ya sha a-ji-garau, ba zai yi gagau ba.

Sauran waɗanda ake raɗe-raɗi a kan su, sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

* Kada a manta, ana zargin Tinubu cewa ɗuwawun sa jaɓe-jaɓe su ke da kashin rashawa tun shekaru da dama. Sannan kuma kuɗin da ya haifa a cikin motoci biyu a jajibirin zaɓen 2019, sun zama makaman yi masa yarfe ta ko ina a yanzu.

* A wani binciken ji ra’ayi da aka bayyana cikin 2019, a lokacin kashi 35 ne na ‘yan Najeriya su ka nuna don komawa wasu ƙasashen waje kacokan daga Najeriya.

* A binciken 2021 kuwa, kashi 70 bisa 100 na waɗanda aka tambaya ke sha’awar bari Najeriya.

* Rashin kwanciyar hankali da tashin-tashinar juyin mulkin da ake fama a za su iya shafar zaɓen 2023. Misali idan aka dubi juyin mulkin Burkina Faso ya kaɗa hantar shugabannin Najeriya, su na tunanin kada fa guguwar juyin mulki ta shigo Najeriya.

* Dalilan da sojoji suka bayar kafin shi juyin mulki a Burkina Faso sun haɗa da kasa kawo ƙarshen ta’addanci da ya yi salwantar dubban rayuka da ɗimbin dukiya, a Najeriya haka abin ya ke.

* ‘Yan ta’adda sun kashe sama da mutum 7,500 a Najeriya cikin shekaru shida kuma sun kori sama da mutum miliyan 1.6 daga gidajen su.

* Rashin yawan masu fita su na jefa ƙuri’a da kuma irin yadda ake gadanƙarma a sakamakon zaɓe na ci gaba da ƙara jefa Najeriya wani hali mai nuna miƙa mulki daga wannan
gwamanti zuwa sabuwa ba zai yi wani armashi ba.

* Teniola Tayo, wadda ita ce Babbar Mai Bincike a Cibiyar Nazarin Tsaro na Afrika ta Yamma, Sahel da Tafkin Chadi, ta yi wannan bincike ne da haɗin guiwar Gwamantin Netherlands.