Ko ASUU za ta bi umarnin kotu ta koma bakin aiki?

Kotun daukaka kara a ranar Juma’a, ta umurci kungiyar malaman jami’o’i, ASUU da ta gaggauta janye yajin aikin da take yi a wani sharadi na kotun kafin karbar bukatar kungiyar ta daukaka kara kan hukuncin da kotun Da’ar Ma’aikata ta kasa ta yanke wanda ya umarci kungiyar ta janye yajin aikin.

Kotun ta amince da bukatar ne bisa sharadin cewa kungiyar ta yi biyayya ga hukuncin da karamar kotun ta yanke sannan kuma ta janye yajin aikin nan take har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.

Kotun ta baiwa ASUU wa’adin kwanaki bakwai da ta sake daukaka kara kan bin hukuncin da karamar kotu ta yanke.

  • Yajin Aiki: “Ina da kwarin gwuiwa kan matakin da Buhari zai dauka kan ASUU” Gbajabiamila

  • Ko ASUU za ta bi umarnin kotu ta koma bakin aiki?

Sai dai ko ASUU za ta bi umarnin kotu?

Jim kadan bayan hukuncin kotun Kungiyar ta bayyana cewa ta tuntubar lauyoyinta domin duba yiwuwar bin umarnin kotun.