KAZAFIN SATA: Kotu ta yanke wa tsohon kansila hukuncin biyan sama da Naira miliyan 4 ga matan da ya sa ta yi rawa zindir a bainar jama’a

Babban kotu a Uyo jihar Akwa-Ibom ta yanke wa wani tsohon kansila hukuncin biyan Naira miliyan 4.2 ga matar da ya sa ta yi rawa zindir a bainar jama’a.

Lauyan da ya shigar da kara Inibehe Effiong ya bayyana cewa Uduak Nseobot da matarsa Aniedi sun ci zarafin Iniubong Essien saboda suna zarginta da sace kudaden da aka lika musu a lokacin auren su da suka yi tun a shekarar 2018.

Effiong ya ce Nseobot da Anirdi sun yi garkuwa da Iniubong zuwa kauyen da yake wakilta a karamar hukumar Ibiono Ibom inda suka sa Iniubong ta cire kayanta tas suka shafa mata baking gawayi a jikinta sannan suka daura mata igiya a kugunta suna janta cikin unguwanni tana rawa suna dukanta.

Lauyan ya ce duk da cewa Iniubong ta yi tsawon shekaru 10 tana kawa da Anirdi sannan ta musanta aikata haka amma sai da Nseobot da Anirdi suka ci zarafinta.

Alkalin kotun Edem Akpan ya ce hakan da suka yi ya nuna yadda ‘yan siyasa ke wulakanta mutanen da suka zabe su.

Akpan ya ce a dalilin haka Nseobot da Anirdi za su biya Iniubong Naira miliyan 4.2.

Effiong ya ce zai yi kari wajen ganin Nseobot da Anirdi sun gudanar da hukuncin da babbar kotun ta yanke koda Nseobot da Anirdi sun amince su daukaka kara.