KATSINA DAI: ‘Yan bindiga sun kashe mutum hudu a Barawa, Karamar Hukumar Batagarawa

Akalla mutum hudu ne suka gamu da ajalinsu a dalilin harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Barawa dake karamar hukumar Batagarawa jihar Katsina.

Kauyen Barawa na da nisan kilomita 10 daga Babban Birnin jihar.

Wani mazaunin kauyen Bashir Isa ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa mahara sama da 100 ne suka shigo kauyen da karfe Tara na daren Lahadi.

Isa ya ce sun shigo suna ta harbi ta ko ina a dalilin haka mutum hudu suka mutu sannan da dama suka ji rauni a jikinsu.

“Daga ciki akwai maza uku da wata dattijiya daya da maharan suka kashe.

Ya ce bayan haka maharan sun saci dabobbi da abinci daga shaguna da gidajen mutane a kauyen.

Wani mazaunin kauyen da baya so a fadi sunan sa saboda tsaro ya ce maharan sun karbi Naira 400,000 daga hannun wani Malam Bello Musa a kauyen.

“Tuni mun yi jana’izar mutum hudu din da aka harbe sai dai ba zan yi mamaki ba idan wani ciki wadanda suka ji rauni ya mutu da yamman yau ba.

Zuwa lokacin da aka rubuta labarin rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce komai ba amma gwamnatin jihar ta tabbatar da harin da maharan suka kai kauyen Barawa.

Kwamishinan wasanni Sani Danlami ya ce gwamnati ta aika da kudade da buhunan shinkafa domin tallafawa ‘yan uwan mutanen da suka rasa rayukan su da dukiyoyinsu a wannan harin.

Ya ce gwamnati baiwa wadanda suka rasa dukiyoyinsu naira 50,000 kowannen su sannan su kuma wadanda suka rasa wani nasu an hada musu da buhun shinkafa d akan naira 50,000 din kowannen su.

Jihar Katsina na cikin jihohin Arewa dake yawan fama da hare-haren ‘yan bindiga a kasar nan.

Domin dakile aiyukkan maharan gwamnatin jihar ta yanke layukan sadarwa, ta Hana siyar da man fetur a galan sannan ta rufe wasu kasuwani da ake ci mako-mako.

Duk da haka ‘yan bindiga ba su daina Kai wa mutane hari ba a jihar.