KATSINA DAI: ‘Yan bindiga sun buɗe wa motar fasinja wuta, sun bindige biyar a cikin su

An bada rahoton cewa ‘yan bindiga sun bindige fasinjoji biyar tare da ji wa wasu uku rauni, a lokacin da su ka buɗe masu wuta tsakanin ‘Yan Tumaki da Ɗanmusa, cikin Jihar Katsina, a ranar Asabar da safe.

Ƙaramar Hukumar Ɗanmusa na ɗaya daga cikin yankunan da ‘yan bindiga su ka hana zaman lafiya a Jihar Katsina, kuma ta haɗa iyaka da Dajin Rugu, Safana, Ƙanƙara da wasu ƙauyukan Jihar Zamfara.

Wani ganau ɗin waɗanda aka buɗe wa wutar mai suna Musa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa fasinjojin da aka buɗe wa wutar sun dawo ne daga Benin, Babban Birnin Jihar Edo, ɗaya kuma ya dawo ne daga Abuja inda ya je ya kai kaji.

Ya ce waɗanda aka buɗe wa wutar ‘yan ƙauyen Gobirawa ne da Kaigar Malamai cikin Jihar Katsina.

“Motar da su ke ciki ƙirar Golf ce. Ta tashi daga ‘Yan Tumaki da niyyar zuwa Ɗanmusa da safe. Fasinjojin sun kwana ne a ‘Yan Tumaki saboda sun isa garin cikin talatainin dare. Da safe sai suka hau motar ƙirar Golf domin ta ƙarasa da su Ɗanmusa, inda daga can za su hau babura zuwa ƙauyukan su.

“Amma sai aka kai wa motar farmaki, aka buɗe mata wuta, mintuna kaɗan bayan ta bar ‘Yan Tumaki.

“Abin da ya faru shi ne, ‘yan bindiga sun hango motar tafe, su ka tsayar da direban, ya ƙi tsayawa. Sai suka buɗe wuta, motar ta riƙa hantsilawa, har ta je ta yi karo da bishiya.” Inji Musa.

Musa ya ce ko da ‘yan bindiga su ka ga motar ta faɗi, sai su ka gudu ba su tsaya ba.

“Wasu mutane da suka kai ɗaukin gaggawa sun kira ‘yan sanda a Ɗanmusa, suka ɗauki gawarwakin da sauran mutum ukun da su ka ji raunuka zuwa asibiti. Tuni mun rufe gawarwakin, masu ciwukan kuwa na asibiti.” Cewar Musa.

Wata majiya kuma ta ce an kai masu hari ne saboda haushin sojoji da ‘yan sanda sun hana ‘yan bindigar kai wani mumnunan hari na satar shanu a ranar Alhamis.

“Yan bindigar har sun yi nasarar kwace shanu, amma jami’an tsaro su ka bi su su ka ƙwato shanun, har aka kashe wasu ‘yan bindigar.” Inji shi.

Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Katsina, Gambo Isa bai yi magana ba tukunna.