KATSINA A HANNUN ƳAN BINDIGA: Mahara sun yi garkuwa da Dagacin Banye, yankin Charanci

Ƴan bindiga sun yi tattaki cikin dare a ranar Juma’a, su ka dira Banye, inda su ka yi gaba da Maigarin Banye, Bishir Giɗe.

Banye ta na cikin Ƙaramar Hukumar Charanci, kuma ta yi iyaka da garin Barkiya ta ɓangaren Ƙaramar Hukumar Kurfi.

Wani ɗan jarida mai suna Nura Ishaq da ke Katsina, wanda ɗan uwan basaraken ne, ya tabbatar da labarin, kuma ya ƙara da cewa zuwa yanzu ba a tantance yawan waɗanda aka tafi da su ba, saboda yanke wayoyin sadarwa a cikin jihar.

Haka kuma ba a ji ɗuriyar halin da ake ciki ba tun bayan tafiya da Bishir Giɗe, saboda katse wayoyin sadarwa a wasu sassan jihar Katsina.

Kakakin Yaɗa Labaran Masarautar Katsina, ya shaida wa wakilin mu cewa ya samu labarin an yi garkuwa da Maigarin Banye, amma babu wani ƙarin haske tukunna daga jami’an tsaro zuwa ga masarautar Katsina.

Ya sanar da wakilin mu cewa da zarar ya samu rahoto, zai yi masa ƙarin haske.

Duk da ana ganin yankin Charanci babu dazuka, ana mamakin yadda aka yi tattaki a ƙasa har cikin Banye a yi garkuwa da mutane.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES Hausa cewa bayan mahara sun tafi da Bishir Giɗe, jama’a sun bi sawun su inda aka gano cewa nausawa kudu aka yi da shi, kuma a ƙasa, ba bisa babura ba.

“An bi sawun su har kusa da Rawayau, daga nan kuma aka rasa inda su ka yi.” Inji majiyar.

Watannin baya a cikin Ƙaramar Hukumar Charanci an yi garkuwa da Dagacin Radda.