KASUWAR GWAL A KANO: Najeriya za ta magance asarar dala biliyan 9 da ake yi a haƙar zinari duk shekara

Najeriya ƙasa ce da Allah ya albarkace ta da ma’adinai, waɗanda su ka haɗa har da masu tsadar gaske da duniya ke tinƙaho da su.
An ƙiyasta akwai metrik tan 200 a ƙarƙashin ƙasa na gwal, wanda ya na ɗaya daga cikin albarkatun ƙasa bakwai da ɓangaren ma’adinan Najeriya ta ɗaura banten maida hankali ana haƙowa tare da cin moriyar su.
Baya ga fetur da gas, zinari shi ne mafi daraja a cikin ƙasar nan. Wannan zinari da ke cikin ƙasar Najeriya ya samu karɓuwa sosai a duniya.
Domin wani rahoto ya nuna cewa a yankin Maru cikin Jihar Zamfara, can ne ake kallo wata aljannar masu hada-hadar zinari.
Sai dai kuma duk da cewa zinari ɗimbin dukiya ce mai haɓaka tattalin arzikin ƙasa, a Najeriya wannan ma’adinai mai tsada ya zama mugun abu.
Akasari masu haƙar zinari a Najeriya sun karkata wajen aikata muggan laifukan da su ka haɗa da danne haƙƙin masu haƙƙi, sumogal, tirsasa yara aikin ƙarfi, kashe-kashe, illolin lahanta lafiyar jiki da sauran su.
Cikin 2018 an samu sanduƙin zinari 315, sannan kuma Jihohi 8 sun haƙo ma’aunin zinari 1212.77, inda a Jihar Osun da Neja su ka samar da kashi 70.36.
Daga cikin naira biliyan 2.5 da gwamnati ta samu kuɗin konon zinaria cikin 2018.
Cikin shekarar 2019 an samu har 2,586, inda aka bayar da lasisin haƙo zinari 1,141.
Sai dai an danganta rashin samun haraji mai yawa daga zinare, musamman saboda ayyukan masu haƙo shi ba da izni ba.
Najeriya ta na asarar dala bilyan 9 a duk shekara saboda masu sumogal ɗin.
Sanata Orji Uzor Kalu ya taɓa yin kira a yi bincike kan maƙudan kuɗaɗen da gwamnati ke asara saboda masu harƙallar zinari.
An kuma tabbatar da cewa ayyukan haƙar zinari ta haramtacciyar hanya ya taimaka sosai wajen ruruta fitinar ‘yan bindiga a jihohin Arewa maso Yamma, inda garkuwa da mutane ya yi kaka-gida.
Ana ganin ana amfani da ma’adinan ne ana karɓar makamai a yankunan.
Wani rahoto da EnactAfrica ta fitar, ya nuna cewa an yi asarar rayuka 6,319 a jihar Zamfara daga 2011 zuwa 2019 ta musabbabin rikice-rikicen da ke da alaƙa da laifukan haƙar ma’adainai.
Yayin da a 2010 mutum 400 suka kamu da cututtukan gubar ma’adinai a Jihar Zamfara.
Cikin 2015 kuma gubar ma’adinai ta kashe mugun yara 28 a Jihar Neja.
Sai dai kuma a yanzu an yunƙuro da ƙoƙarin kafa kasuwar hada-hadar zinari a Kano.
Kasuwar mai suna Kano Gold Souk, idan aka kammala ta za ta zama irin ta ta farko a Afrika.
Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano da Karamin Ministan Harkokin Ma’adinai Uchechukwu Ogah, sun bayyana ƙoƙarin gina kasuwar cewa ya yi daidai da lokacin da aka fi buƙatar kasuwar.