KASUWA A KAI MAKI DOLE: Hada-Hadar Kasuwanci A Tashar Baga Da Ke Jihar Borno, Maris 12, 2023

Shirin Kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya kai ziyara Tashar Baga, wacce ta rikide ta koma kasuwar hada-hadar kifi da sauran wasu kayayyaki. 

‘Yan kasuwar sun yi bayani kan harkar kasuwancinsu da kuma yadda sauya fasalin Naira da gwamnatin Najeriya ta yi ya shafi harkokin cinikayyarsu sosai. Bayan haka ‘yan kasuwar sun yi fatan a yi zaben gwamoni a Najeriya a gama lafiya.

Saurari cikakken shirin da Haruna Dauda Ya gabatar: