KASAFIN ‘KURAYEN’ 2022: Ɗan Majalisa ya ce Naira biliyan 134 ta yi masu kaɗan

Duk da kuka da ƙorafin da jama’a ke yi a kan yawan kuɗin da aka ware wa Majalisar Tarayya har Naira Biliyan 134, shi kuwa Kakakin Majalisar Tarayya Honorabul Ben Kalu cewa ya yi kuɗin sun yi kaɗan matuƙa.

Daga nan sai ya yi kira da a ƙara kamfatar maƙudan kuɗaɗe masu kauri a ƙara gabza masu, “domin Majalisa ta ji daɗin gudanar da aikin ta yadda ya kamata.”

Ben Kalu ya yi wannan furuci a wurin mahawarar tattauna kasafin Naira tiriliyan 16 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar kwanan baya.

A cikin kasafin dai kusan Naira tiriliyan 6 duk bashi ne za a ciwo domin a gudanar da aikin.

Ba wannan ne karo na farko da Ben Kalu ya fara raina kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke kashewa a Majalisar Tarayya da ta Dattawa ba.

Cikin watan Fabrairu ma sai da Ben Kalu ya ce Majalisar Najeriya ita ce mafi tsiyacewa da talauci a duk duniya.

Bayan wata ɗaya sai ya sake fitowa ya ce Majalisa na fama da ƙarancin kuɗi, don haka a sake nazarin abin da ake bata, domin a yi ƙari.

Yayin da ake faman faɗi-tashin ciwo bashi, a gefe ɗaya kuma majalisa na neman ƙari. Sannan kuma majalisar ta ƙi amsa kiraye-kirayen jama’a cewa ta riƙa fito a jadawalin yadda ta ke kashe kuɗaɗen da ake bata, domin a riƙa bin diddigin ta.

A yayin mahawarar, Kalu ya ce Majalisa ba ta amfana da ko sisi ba, daga Naira biliyan 280 da aka yi ƙari cikin kasafin 2022 a cikin kuɗaɗen da ake rarrabawa ga ɓangarorin gwamnati.

A wata sabuwar kuma, PREMIUM TIMES Hausa ta buga yadda Buhari da Obasanjo za su kashe naira biliyan 3.6 wajen narkar abinci da zirga-zirga kaɗai.

Kasafin Naira Biliyan 3.6 da Shugaba Muhammadu Buhari ya ware wa kan sa tare da Mataimakin sa Yemi Osinbajo, waɗanda za su kashe wajen cin abinci da tafiye-tafiye, shi ne mafi tsada da Buhari ya ware, tun daga shekarar 2015 har zuwa wannan shekara.

Buhari ya ware wa ofishin sa Naira biliyan 2.6, sai Naira miliyan 778 kuma ya ware wa ofishin mataimakin sa, Yemi Osinbajo.

Tafiye-tafiyen shugaban ƙasa zai lashe Naira biliyan 2.3, waɗanda a ciki za a kashe naira miliyan 775.6 a zirga-zirgar cikin gida Najeriya. Sai kuma Naira biliyan 1.5 da za ta tafi wajen zirga-zirgar ƙasashen waje.

Zirga-zirgar Mataimakin Shugaban Ƙasa za ta ci Naira 778, adadin da idan aka rarraba su, Naira miliyan 301 za su tafi wajen tafiye-tafiye a cikin Najeriya, Naira miliyan 476 kuma wajen tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare.

Jama’a da daman gaske su na mamakin yadda Buhari zai kashe miliyan 775 a tafiye-tafiyen cikin gida.

Da yawa na cewa ai ba ya zuwa ko’ina. Idan ka ga ya je wata jiha, to lakcin kamfen ne domin ya taya gwamnan APC mai mulki a jihar kamfen ɗin cin zaɓe.

“Mutumin nan fa ko duba wasu manyan ayyuka da aka yi ko ake kan yi ba ya zuwa. To a ina zai kashe Naira miliyan 775 kuma?

Haka kuma ana sukar Buhari ganin yadda duk nisan ƙasa, ba ya jin wahalar zuwa taro. Sannan kuma duk kusancin wani gagarimin aiki a Najeriya, Buhari ba ya zuwa ya duba yadda aiki ke tafiya.

A kasafin 2018, Buhari ya ware Naira biliyan 1.52 domin kashe wa ofishin sa kason cin abinci da zirga-zirga. Cikin 2019 ya ware Naira biliyan 1.5.

Son Kai Ba Kishin Talakawa Ba:

Buhari ya ware wa asibitin fadar sa naira biliyan 21.9, Manyan Asibitocin Najeriya 14 kuma naira biliyan 19.17.

Ana ce-ce-ku-ce da cacar-baki a kan maƙudan kuɗaɗen da Buhari ya shigar a kasafin 2022, domin kashewa wajen gina sabon Asibiti Sashen Shugaban Ƙasa a Fadar Aso Rock, wanda za a kashe wa Naira biliyan 21.9.

Asibitin dai idan an kammala shi nan da shekara biyu, zai riƙa kula da Shugaban Ƙasa da iyalin sa, Mataimakin Shugaban Ƙasa da iyalin sa, sai kuma sauran manyan ƙusoshin gwamnatin tarayya.

Babban abin damuwa dangane da waɗannan maƙudan kuɗaɗen da za a kashe, shi ne ganin yadda idan an haɗa kuɗaɗen da Buhari zai kashe a Manyan Asibitocin Najeriya 14, wato Federal Teaching Hospital, ba su ma kai adadin waɗanda za a kashe a asibitin Fadar Shugaban Ƙasa ba.

Wannan ya janyo ana kukan cewa Buhari bai damu da inganta rayuwar ‘yan Najeriya ba.

Sannan kuma ana kukan yadda kasafin bai bada fifiko ga harkokin ilmi da kiwon lafiya ɗungurugum ba.

Da wahala wannan asibiti da za a gina a Fadar Shugaban Ƙasa ya zama dalilin daina fitar Buhari zuwa Landan, domin duba lafiyar sa. Saboda sai nan da shekaru biyu za a kammala ginin, wanda a lokacin ki dai Buhari ya fara yin bankwana da kujerar mulki, ko kuma ya kammala ya koma Daura da zama.

Kafin Buhari ya nemi amincewar Majalisar Dattawa da ta Tarayya domin kashe Naira biliyan 21.9 wajen gina asibiti a cikin Fadar sa, a shekarar da ta gabata an kashe Naira biliyan 1.4 a wajen aikin asibitin.

Babban Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa, Usman Tijjani ya bayyana wa sanatocin da su ka kai ziyara asibitin a cikin Agusta cewa, idan aka kammala shi, zai kasance manyan jami’an gwamnati da iyalan shugaban ƙasa da na mataimakin sa da su kan su Shugaba da Mataimaki, duk a wurin za a riƙa duba lafiyar su.

Wannan kasafin asibitin fadar Buhari ya haura na manyan asibitocin Najeriya 14 (Federal Teaching Hospitals) yawa da Naira biliyan 2.7 kenan.