Kano ta wayi gari da rasuwar dattijo Muktar Adnan, Sarkin Ban Kano

Birnin Kano da kewaye, musamman garin Ɗambatta, an tashi da rasuwar Muktar Adnan, Sarkin Ban Ɗambatta.

Adnan ya rasu a ranar Juma’a, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Ya rasu ya na da shekaru 95, kuma shi ne mafi daɗewa daga cikin ‘Yan Majalisar Hakimai Masu Naɗa Sarki a Kano, wato ‘kingmakers’ a Turance.

Shi ya naɗa wa sarakunan Kano huɗu rawanin sarauta, ciki kuwa har da Sarki Ado Bayero, cikin 1963.

Sarki Sanusi I ne ya naɗa shi Sarkin Ban Kano, kuma Hakimin Ɗambatta, cikin 1954.

Sai dai kuma Gwamna Abdullahi Ganduje ya tsige shi tare da Hakimin Tsanyawa, Bichi, Dawaki Tofa da na Minjibir, a lokacin da su ka ƙi goyon bayan ƙirƙiro sabbin masarautu a Kano, cikin 2019.

Daga nan ya dawo gidan sa a Kano cikin unguwar Dambazzau ya ci gaba da zama, har rasuwar sa a ranar Juma’a.

Za a yi jana’izar sa yau bayan Sallar Juma’a a garin Ɗambatta.

Gogaggen masanin tarihin sarautar Kano, kuma ɗan jarida Fatuhu Mustapha, ya shaida wa Premium Times Hausa cewa, Muktar Adnan shi ne Kwamishinan Ilmi na farko a Kano, cikin 1968.

Shi ne mahaifin toshon Ministan Harkokin Kuɗaɗe, Mansur Muktar.

Shi ne Hakimi mafi daɗewa a tarihin Kano, ko a ce a tarihin Arewa ma.

Ya gaji mahaifin sa, Sarkin Bai Adnan, wanda aka bayyana Adnan da cewa, wani gogaggen mutum ne mara kasala.

Mahaifin sa ne ya fara hakimcin Dambatta, tun bai zama Sarkin Bai ba, ya na Dammaje Hakimin Babura, aka dawo da shi Dambatta, bayan an cire Sarkin Bai Abdulkadir daga Hakimin Danbatta. amma aka bar masa sarautar sa, saboda samun sa da sakaci da sha’anonin mulki da na shari’a.

Yana Hakimin Dambatta, Sarkin Ban Kano, aka yi masa Kwamishinan ilmi na Jihar Kano na farko cikin 1968.

Shi ne ya fara ƙirƙiro da Kano Hukumar Tallafin Kuɗaɗen Ɗaliban Jihar Kano, wato, Scholarship Board, Kano State Polytechnic, Audu Bako School of Agric da wasu manyan makarantun sakandire a Jihar Kano.

A zamanin sa ilmin boko da na addini ya samu tagomashi ƙwarai.

Saboda himmar sa, an samu yawaitar masu ilmin jami’a daga Kano.

Masarautar Ɗambatta ta samu ɗaukaka ƙwarai dalilin mulkin sa.

Sarkin Kano Bayero ya naɗa shi Sarkin Bai kuma ɗan Majalisar Sarki. Amma har ya rasu ba a taɓa samun sa da wata matsala ba.

Allah ya gafarta masa, amin.