Kannywood ta yi rashin jarumi kuma mai ɗaukan hoto

Rahotanni dake fitowa daga birnin Kano na bayyana rasuwar Jarumi kuma babban mai ɗaukar Hoto a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Ahmad Aliyu Tage, ya rasu.

Jarumi kuma mai bada umarni a masana’antar Ishaq Sidi Ishaq ya tabbatar da rasuwan jarumin.

Hausa Daily Times ta samu labarin cewa jarumin ya rasu bayan fama da gajeruwar jinya.

An wallafa wannan Labari September 13, 2021 2:26 PM