KANJAMAU: Najeriya ce kasar da ta fi yawan jarirai dake dauke da kwayoyin cutar a duniya

Hukumar dakile yaduwar cutar kanjamau ta ƙasa NACA ta bayyana cewa a cikin watanni 18 an gano mutum 350,000 dake dauke da cutar a kasar nan.

Hukumar ta ce tuni wadannan mutane suka fara karban maganin cutar a asibitoci.

Shugaban hukumar Gambo Aliyu ya sanar da haka a taron tattauna inganta hanyoyin kare jarirai daga kamuwa da kanjamau yayin da suke cikin uwayensu.

Aliyu ya ce an gano wasu daga cikin wadannan mutane a yankunan karkara a fadin kasar na.

Sakamakon binciken da NAIIS ta gudanar a shekarar 2018 ya nuna cewa mutum miliyan 1.9 kuma masu shekaru 64 zuwa ƙasa na dauke da cutar a kasar nan.

Aliyu ya ce Dole a mike tsaye wajen inganta matakan kare jarirai daga kamuwa da kanjamau a lokacin da suke cikin Uwayen su tun da wuri.

Ya ce wannan ita hanya daya kuma mafita domin kare jariran dake kamuwa da cutar daga uwayensu.

Aliyu ya ce babban matsalolin dake ci musu tuwo a kwarya shine har yanzu akwai mata Kalla miliyan 6 daga cikin miliyan 8 da basu zuwa awon ciki a lokacin da suke da juna biyu.

“A yanzu haka fama muke da sauran mata miliyan biyu da suke zuwa asibiti don karbar magani.

Ya kuma ce akwai mata da dama da har yanzu basu iya samun kula musamman mazauna karkara.

Ya ce shawo kan wadannan matsaloli zai taimaka wajen kare kiwon lafiyar jarirai daga kamuwa da kanjamau a kasar nan.

Bayan haka Aliyu ya ce duk da haka hukumar ta samu karuwa a yawan mata masu ciki da ke dauke da kanjamau dake karbar magani a asibiti daga 2006 zuwa 2019.

A shekarar 2006 mata masu ciki Kuma masu fama da kanjamau 13,000 ne ke karbar magani a asibiti.

A shekarar 2019 an samu mata 421,000 dake karban magani a kasar nan.

Duk da haka bincike ya nuna cewa Najeriya itace kasar da ta fi yawan jarirai dake dauke da kanjamau a duniya.

Sannan a shekaran 2016 mata masu ciki 160,000 ne ke dauke da cutar a duniya inda daga ciki 37,000 na Najeriya.