KALAMAN ƁATANCI GA ANNABI: Duk wanda ya yi zanga-zangar addini a Kaduna zai ɗanɗana kuɗar sa – Gargaɗin El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Nadir El-Rufa’i ya gargaɗi mutanen Kaduna kada su kuskura su fito yin zanga-zangar addini a jihar
Wannan gargadi na kunshe ne a wata sabarwa wanda Kwamishinan Tsaron Jihar, Samuel Aruwan ya fidda ranar Asabar.
Aruwan ya ce gwamna El-Rufai ya gargaɗi ƴan Kaduna su natsu, su kuma kwantar da hankulan su, kada wani ya kuskura ya shirya zanga-zanga a jihar.
” Akwai raɗe-raɗin da aka samu cewa wasu na shirya zanga-zanga a jihar Kaduna domin kalaman ɓatanci da Debora ta yi akan Annabi SAW. An sanar da jami’an tsaro su kwana cikin shiri.
A karshe gwamnan ya hori shugabanni addini, sarakuna da na alumma su kwantar wa jama’a hankali da isar musu da wannan gargaɗi.