KAI JAMA’A: Jami’an Sibul Difens sun damke wani Uba da Ubansa da suka yi wa ‘ya/Jikan su fyade

Jami’an sibul defens NSCDC a jihar Osun sun kama wani Uba da Ubansa wato kakakan wata yar shekara 13 da suka rika yi wa fyade a gida duk su biyun.

Hukumar NSCDC ta kama wadannan mutane ne bayan yarinyar ta bayyana yadda mahaifinta da kakanta ke danne ta shekaru biyu da suka gabata wa jami’an tsaron.

Kakakin rundunar Adigun Daniel wanda ya sanar da haka ranar Litini a Osogbo ya ce tun a ranar Juma’a jami’an tsaron suka cafke wadannan mutane.

Daniel ya ce yarinyar ta fara zama da kakarta mace daga dangin mahaifiyar ta bayan mahaifiyarta da mahaifinta sun rabu tun tana shekara uku.

“Ta ce da ta Kai shekara biyar sai ta dawo zama da mahaifinta da kakanta namiji.

“Ta ce tun daga wannan lokaci kakanta namiji ya rika lalata da ita.

“A lokacin bata iya fada wa kowa ba saboda karancin shekarunta sannan babu wanda zai yadda da abin da ta fadi.

Daniel ya ce mahaifin yarinyar da ubansa sun karyata abin da yarinyar ta fadi a kansu a ofishin jami’an tsaron.

Ya ce rundunar za ta kai wadannan mutane kotu da zaran sun kammala bincike.

Sannan ita kuma yarinyar an damkata ga ma’aikatar kula da al’amuran mata da yara kanana domin samun kula.

Shugaban hukumar Emmanuel Ocheja ya ce kare hakin yara kanana mata na daga cikin aiyukkan da hukumar za ta fi bada karfi ta a Kai.