Kaddamar da littafi kan ‘Daular Usmaniyya’ – Daga PREMIUM TIMES

A yau Talata ne PREMIUM TIMES ke kaddamar da sabon bugun littafi kan tarihin ‘Daular Usmaniyya’, mai suna ‘Sokoto Caliphate’.

Mai martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamali ne zai jagoranci taron, yayin da ministan matasa da wasanni Sunday Dare, zai kasance babban bako na musamman sannan shugaban Kamfanin Casiva Limited, Nasiru Danu, zai kaddamar da littafin.

Babban Editan jaridar 21st Century Chronicles Mahmud Jega ne, zai yi bitar littafin inda bayan haka zai jagoranci wani bangare na tattaunawa a kan maudu’in “Dangatakar Tarihin Daular Sakkwato a wannan karni da muke ciki a Najeriya a yau.

Jega tare da Farfesa Mukhtar BEllo Bunza da Farfesa Mohammed Junaid za su jagoranci tattaunawar.

An fara buga wannan littafi shekaru 54 da suka wuce a 1967, littafin ‘Sokoto Caliphate’ ya samo asali ne daga kokarin da bincike mai zurfi da wanda farfesa Murray Last yayi a lokacin da yake karatun digirin sa ta PhD a jami’ar Ibada,

Littafin ya yi bincike mai zurfi cikin tarihi a karni na 19 na daular Sakkwato, daular da ta samo asali daga jihadi karkashin jagorancin Usmanu Ɗan Fodio, malamin addinin Musulunci da ya yi fice a karni na 19.

Kafin kutse da mamaye kasashen yankin Afrika ‘mulkin mallaka’ wanda turawa suka yi musamman kasashen Birtaniya da Faransa, daular usmaniyya ya somo tun daga Kasar Kamaru a yanzu zuwa Kasar Burkina Faso ya lula har yankin Agadez zuwa Ilori a Najeriya.

Idan ba a manta ba an soma kaddamar da wannan littafi ne a ranar 1 ga Nuwamba a garin Sokoto, a wajen bukin cikar Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar shekaru 15 kan karagar mulkin sarautar Sarkin Musulmin Najeriya.