Kabilun Irigwe da Fulani sun yi sulhu a Jos

Ƙabilun Irigwe da Fulani da ke zaune a jihar Filato sun amince su yi sulhu a tsakanin su domin samar da zaman lafiya da ci gaban yankin su da karamar hukumar Bassa.

Idan ba a manta ba karamar hukumar Bassa ya dade yana fama da rashin zaman lafiya a dalilin rikicin da rashin jituwa da aka rika samu tsakanin Fulani da ƴan ƙabilar Irigwe.

Kabilun su yi sulhun ne a zaman da suka yi da sarakunan gargajiya da malaman addini wanda kungiyar ‘Dialogue, Reconciliation and Peace (DREP)’ ya shirya.

A wannan zama, shugaban kungiyar kabilar Irigwe Daniel Geh da shugabanin kungiyar makiyaya (MACBAN) Ronku Aka da Muhammad Nuru sun rungumi juna domin nuna sulhun da suka yi.

Geh ya ce kabilar Irigwe a shirye take ta yi zaman lafiya da duk kabilun dake karamar hukumar.

“Tun dama can muna zaman lafiya tsakanin mu da Fulani sannan zaman lafiya zai dawo idan mun ci gaba da zaman lafiya kamar yadda muka yi a da.

Nuru ya yabawa sassantawar da aka yi musamman yadda kabilun suka dade suna rikici a tsakanin su a wannan yankin.

Ya ce za su sanar wa mutanen su game da sulhun da aka yi domin kowa ya koma mazaunin sa a ci gaba da zaman lafiya

Nuru ya yi kira ga gwamnati da ta dauki matakai domin hana barkewar rashin jituwa a tsakanin a bokan zaman nan gaba.