Ka wa Allah ka biya NECO kudin su ko sa sake mana jarabawar mu – Kukan Daliban jihar Kano ga gwamna Ganduje

Dalibai daga wasu manyan makarantun jihar Kano sun yi korafin cewa dalilin kin biya musu kudin jarabawar NECO da gwamnatin Abdullahi Ganduje bata yi ba ya sa hukumar shirya jarabawar NECO ta ki saki musu jarabawar su na bana.

Wasu daga cikin daliban da suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA sun ce suna cikin jimami da hali na takaici ganin takwarorin su dake wasu makarantun da ba na gwamnati ba da ma wasu na gwamnatin da iyayen su suka biya har sun samu guraben ci gaba da karatu a manyan makarantun kasar nan su suna nan zugudum sun zura wa ikon Allah Ido gwamna Ganduje ya ki cewa komai.

” Babu abin da za mu iya yi akai illah mu ci gaba da addu’a ko Allah zai karkato mana da zuciyar gwamna Ganduje ya tausaya mana ya biya hukumar NECO kudin su su sakan mana jarabawar mu. Duka makarantun kimiyya biyar na jihar dalibai na nan suna ta zaman kila wa kala da rokon Allah da kuma mika kukan su ta kowacce hanya domin gwamnati ta waiwaye mu ta biya kudin nan.

” NECO ta ce rabon da gwamnati ta biya su kudin jarabawa tun daga 2018. Gwamnatin Ganduje bata biya kudin jarabawar 2019, 2020, 2021 ba shi yasa ba za su saki jarabawar ba.” In ji wasu daga cikin daliban.

Daliban da ke korafin su sun ce makarantun da wannan rashin sakin jarabawa ya shafa sun hada da makarantun kimiya na Dawakin Kudu, Dawakin Tofa, Gwarzo, Mairo Tijjani da First Lady.

Kurin gwamnatin jihar Kano

Idan ba a manta ba gwamnatin Kano ta fito karara ta rika bugun kirji ta na cewa dalibanta sun yi ragaraga da jarabawar NECO a bana, inda cikin dalibai 89,000 da suka zauna jarabawar, 80,000 sun yi nasarar cinye duka darussa 9.

Kwamishinan ilimin jihar kiru ya bayyana haka cewa maida hankali da gwamnatin Kano ta yi ne akan ilimi ya sa dalibai suka yi nasara kamar yadda ya bayyana.