KAƊA HANTAR PDP: Wike ya gayyaci Gbajabiamila da Gwamnan Legas buɗe ayyukan taya jiha, bai gayyaci ‘yan PDP ba

A daidai lokacin da manyan jam’iyyar PDP ke ta kiciniyar sasanta saɓani tsakanin Gwamna Nyesome Wike da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar, Wike ya gwasale PDP yayin da ya gayyaci Gwamna Babajide Sanwo-Olu ɗan APC na Legas inda ya buɗe wata gadar sama a Fatakwal.
Kwana biyu kuma bayan wannan Wike ya gayyaci Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, inda zai buɗe gidajen ‘yan Majalisar Tarayya da ya gina.
Gwamnatin Wike ta gina gidajen ‘Yan Majalisar Jiha 34 masu ɗakunan kwana huɗu kowane.
Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ne zai taya shi damƙa wa kowane Ɗan Majalisar Jiha na sa makullin gidan.
Wannan lamari dai ya bai wa mutane da dama mamaki, ganin yadda Wike ke rungumar jiga-jigan APC, a lokacin da manyan PDP ke ci gaba da ƙoƙarin ɗinke ɓarakar da ke tsakanin sa da Atiku Abubakar.
A wani labarin rikicin Wike da Atiku kuwa, wani Ɗan Majalisar Tarayya ya bayyana yadda ‘yan barandar Atiku su ka ƙulla tuggun haddasa rikici tsakanin sa da Wike.
Ɗan Majalisar Tarayya Solomon Rob daga Jihar Ribas, ya bayyana cewa wasu ‘yan barandar jikin Atiku Abubakar ne ya haɗa shi rashin jituwa tsakanin sa da Gwamna Wike.
Da ya ke amsa tambayoyi a gidan talabijin na Channels, Rob ya ce, “ƙarairayi da tuggun da makusantan Atiku Abubakar su ka riƙa fesawa kafin zaɓen fidda-gwani da bayan kammala zaɓen ne su ka haddasa rashin jituwa da rashin fahimta tsakanin Atiku da Wike.
“Sun riƙa fesa waɗannan ƙarairayi don kawai su ɓata takarar Wike, kuma su aibata shi bayan ya faɗi zaɓen don kada ya zama mataimakin takara.
Rob ya ce, “da su ke cewa Wike na jin haushin Atiku don bai ɗauke shi ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ba, ƙarya su ke yi, Wike bai faɗi haka ba.
“Kuma shi Wike tun farko takarar shugaban ƙasa ya nema, domin ya na da ajandar sa ta idan ya yi nasara, to ga irin gyaran da zai yi wa matsalolin da su ka addabi Najeriya.”
Rob ya kuma zargi shugabannin PDP na ƙasa da kantara wa Wike ƙarairayi.
Ya ce da ‘yan jagaliyar Atiku ba su yaɗa ƙarairayi kan Wike ba, to da ba a samu wawakeken giɓi tsakanin Wike da Atiku ba.