JIHAR NEJA TA KAMA WUTA: Mahara sun kashe sojoji 30, mobal 7, farar hula da dama

Mummunan bayanin da ke fitowa daga Jihar Neja ya tabbatar da kisan aƙalla sojoji 30, ‘yan sandan mobal 7 da kuma farar hula da dama, a wani ƙazamin farmaki da mahara su ka kai wani wurin haƙar ma’adinai da ke cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da cewa an kai mummunan harin, kuma ta ƙara da cewa har yanzu ba ma tabbatar da ko adadin yawan waɗanda aka kashe ɗin ba.
Mazauna yankin da aka kai farmakin sun tabbatar da cewa sune waɗanda su ka fita tsintar gawarwaki baya ƙura ta lafa, sun ɗauko gawarwakin sojoji 30 da kuma da mobal 7 a cikin dajin da ke kewaye da wurin haƙar ma’adinan a safiyar Alhamis.
Haka kuma an tabbatar da kwaso gawarwakin fararen hula shida a cikin daji.
Mazauna yankin sun ƙara da cewa maharan sun kwashi mutane da dama ciki har da ‘yan Chana, su ka arce da su a ranar Laraba.
Wani jagoran matasa a Shiroro mai suna Yusuf Kokki, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mazauna yankin sun gani kuma sun ji lokacin da maharan ke wa wurin haƙar ma’adinan zabarin ruwan wuta da muggan makamai.
“A yanzu haka a kowane lokaci yawan waɗanda aka kashe a harin wanda aka kai Ajata-Aboki sai ƙaruwa ya ke yi. Domin zaman yanzu dai iyar gawarwakin da aka tsinto har da na sojoji 30 ne.”
Kokki ya ce ana sa ran ƙara gano wasu gawarwakin, saboda har zuwa safiyar ranar Alhamis masu ceto na ci gaba da neman gawarwaki a cikin jeji.
Ya ce maharan sun dira wurin haƙar ma’adinan, wadda mallakar wasu ‘yan Chana ce, inda su ka buɗe wa ma’aikata da masu tsaro wuta.
Ya ce tun a wurin haƙar ma’adinan take aka bindige mobal 7, da farar hula 6.
“Sojojin da aka girke a garin Erena su ka garzaya wurin domin kai ɗaukin gaggawa, inda ba su ankara sai mahara su ka afka masu da harbi, inda aka bindige sojojin Najeriya da dama.”
Da yawan waɗanda aka ji wa ciwo kuma an garzaya da su asibiti domin kula da su.
Kwamishinan Harkokin Tsaro na Jihar Neja, Emmanual Umar, ya ce artabun da aka yi da sojoji ya sa sojojin sun ceto jama’a da dama da hannun mahara.