Jihar Jigawa: Yadda suke kallonta da yadda muka kallonta, Daga Adamu Mai-Ɗalibai Kazaure

Jihar Jigawa ɗaya ce daga cikin Jihohi 36 na Tarayyar Najeriya, an ƙirƙireta daga cikin Jihar Kano a shekarar 1991.

Wasu suna ganin kamar an ware wasu Ƙananan Hukumomi na Jihar Kano waɗanda suka fi koma baya, sannan kuma sai aka yi haɗakar wasu Masarautu (masu Tarihin Tutar Shehu Usmanu Danfodiyo) don a samar da Sarkin Kano guda ɗaya a cikin Jihar Kano guda ɗaya.

Ƙirƙirar Jihar Jigawa ya sa an ƙara samar da wasu sababbin Masarautun a cikin sabuwar Jihar dai, wanda hakan ya haifar da kallon wasu daga cikin mutanen Jihar ya koma kallon Masarautun ba kallon Jiha ba, sakamakon hakan sai ya haifar da rabon komai na Jihar ana kallonsa da idon Masarautu ba da idon Jiha ba. Mu ajiye wannan kallon a gefe (zamu tattauna akai wani lokacin in Allah Ya so)

Daga wani gefen, wasu suna kallon Jihar Jigawa a matsayin Jiha mafi koma baya a tattalin arziki inda har a wani lokaci an taɓa cewa Jihar ta fi kowace Jiha Talauci a Tarayyar Najeriya.

Haka suke kallonta, mu kuma muna kallonta a matsayin Jiha da Allah Ya shimfiɗa Ƙasar Noma (Rani da Damina) ga kuma Jarin Tarin Al’umma waɗanda zasu iya amfana da arzikin da Allah Ya ajiye a inda ya haliccesu in da a ce an ɗorasu akan hanyar neman arzikin.

Ba zai taɓa yiwuwa ba a ce ga Arziki Allah Ya saukar da shi kuma a ce Talauci ya zauna a waje, sai dai idan an samu Jahilci ya kai ziyara wajen da Allah Ya shimfiɗa arzikin ne.

Idan aka juya ta wani ɓangaren kuma, wasu suna kallon Jihar Jigawa a matsayin Jiha da rarrabuwar kawunan al’ummarta da ƙauyancinsu ba zasu taɓa bari su samu wani cigaba mai ɗorawa ba, mu kuma muna kallon a wannan Tarayyar ta Najeriya da wahala ka samu wata Jiha da ke da al’umma masu Addini da al’adu iri ɗaya kamar Jiharmu ta Jigawa mai albarka.

Akwai masu yiwa Jigawa kallon Jihar da ko Babban Birnin Jiharsu ma Ƙauye ne ballantana sauran ƙananan hukumominsu, mu kuma muna kallon idan zamu samu damar damawa insha Allahu zamu iya mayar da Birnin Dutse kamar irin ƙaramin birnin Abu-Dhabi ko kuma Birnin Doha domin kuwa waɗannan bishiyoyin Dabinon da Duwatsun fasahar zamani kawai suke buƙata ‘yar kaɗan,yazunnan zaka ga ana tururuwa wajen yawon buɗe ido a Jigawar tamu.

A cikin Jihar Jigawa ne fa muke da ƙasar Noma ta Fadama, a wani gefen kuma muke da ƙasar Sahara, a cikinta ne muke da Duwatsu a wani ɓangaren kuma ga Dazuzzuka, a cikinta ne muke da Dama-Damai wani wajen kuma ga Koguna. Haba Jama’a!! Bai dace ba a zauna hakanan a zura idanu, ga ƙoshi ga kwanan yunwa? Ko kuma Kaza kwana kan dame?

Don Allah a samu wasu su canja wannnan kalle-kallen, ana yin aikin gayya labarin zai canja.