JANA’IZAR SARKIN BAI: Ganduje da maƙarraban sa sun ƙaurace wa jana’zar marigayin

Ranar Juma’a ce garin Ɗambatta ya cika da ɗimbin jama’a da su ka halarci jana’izar Sarkin Ban Kano, Muktar Adnan.

Adnan ya rasu bayan fama da rashin lafiya a Kano ya na da shekaru 95.

Premium Times Hausa ta bayar da labarin rasuwar da irin gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa Jihar Kano.

Adnan shi ne mafi daɗewa a cikin ‘Yan Majalisa Masu Naɗa Sarki (Kingmakers).

Ya nada wa Sarakuna huɗu rawani a Kano, ciki har da Sarki Ado Bayero cikin 1963.

Sai dai kuma Gwamna Ganduje ya cire shi tare da Hakimin Bichi, Minjibir da Dwakin Tofa, saboda sun nuna adawa ga daddatsa Masarautar Kano gida biyar da Ganduje ya yi a cikin 2019.

Sai dai kuma a yayin jana’izar, PREMIUM TIMES HAUSA ta kalato cewa Gwamna Ganduje bai je ba, kuma bai tura wakili ko ɗaya ba.

Haka sauran dukkan muƙarraban Ganduje babu wanda ya halarta.

Wani mutumin Ɗambatta mai suna Abdullahi Ɗan Waziri, ya rubuta cewa, “Abin mamaki duk da cewa Kakakin Majalisar Kano da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnanti daga Makoɗa suke, garin da a baya ƙarƙashin Masarautar Ɗambatta ya ke, amma babu wanda ya halarta daga cikin jami’an gwamnatin Kano. Kai ko mashawarci ko mai taimakawa Ganduje bai tura ba.”

A na sa ɓangaren, Sarkin Kano (Murabus) Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi wani rubutu mai ratsa jiki a kan rashin Muktar Adan.